Revelation 7 (BOHCB)
1 Bayan wannan, na ga mala’iku huɗu, a tsaye a kusurwoyi huɗu na duniya, suna tsare iskoki huɗu na duniya, domin su hana wani iska hurawa a bisan ƙasa ko a bisan teku ko a bisa wani itace. 2 Sai na ga wani mala’ika yana zuwa daga gabas, yana da hatimin Allah mai rai. Ya yi kira da babbar murya wa mala’ikun nan huɗu da aka ba su iko su cuci ƙasa da teku ya ce, 3 “Kada ku cuci ƙasa ko teku ko kuma itatuwa sai bayan mun sa hatimi a goshin dukan bayin Allahnmu.” 4 Sai na ji yawan waɗanda aka sa musu hatimi. Su 144,000 daga dukan kabilan Isra’ila. 5 Daga kabilar Yahuda mutum 12,000 ne aka sa musu hatimin,daga kabilar Ruben mutum 12,000,daga kabilar Gad mutum 12,000, 6 daga kabilar Asher mutum 12,000,daga kabilar Naftali mutum 12,000,daga kabilar Manasse mutum 12,000, 7 daga kabilar Simeyon mutum 12,000,daga kabilar Lawi mutum 12,000,daga kabilar Issakar mutum 12,000, 8 daga kabilar Zebulun mutum 12,000,daga kabilar Yusuf mutum 12,000,daga kabilar Benyamin mutum 12,000. 9 Bayan wannan sai na duba, can a gabana kuwa ga wani taro mai girma, wanda ba mai iya ƙirgawa, daga kowace al’umma, kabila, mutane da kuma harshe, suna tsaye a gaban kursiyin da kuma gaban Ɗan Ragon nan. Suna saye da fararen tufafi suna kuma riƙe da rassan dabino a hannuwansu. 10 Suka tā da murya da ƙarfi suna cewa,“Ceto na Allahnmu ne,wanda yake zaune a bisan kursiyi,da kuma na Ɗan Ragon.” 11 Dukan mala’iku suna tsaye kewaye da kursiyin da kuma kewaye da dattawan tare da halittu huɗun nan masu rai. Suka fāɗi da fuskokinsu ƙasa a gaban kursiyin suka kuma yi wa Allah sujada, 12 suna cewa,“Amin!Yabo da ɗaukaka,da hikima da godiya da girmada iko da ƙarfisun tabbata ga Allahnmu har abada abadin.Amin!” 13 Sai ɗaya daga cikin dattawan ya tambaye ni ya ce, “Waɗannan da suke saye da fararen tufafi su wane ne, daga ina kuma suka fito?” 14 Na amsa na ce, “Ranka yă daɗe, kai ka sani.”Sai ya ce, “Waɗannan su ne waɗanda suka fito daga matsananciyar wahala; sun wanke tufafinsu suka kuma mai da su farare da jinin Ɗan Ragon nan. 15 Saboda haka,“suna a gaban kursiyin Allahsuna masa hidima dare da rana a cikin haikalinsa;kuma wannan mai zaune a kursiyin zai shimfiɗa tentinsa a bisansu. 16 ‘Ba za su sāke jin yunwa ba;ba za su kuma sāke jin ƙishirwa ba.Rana ba za tă buga su ba,’ko kuma kowane irin zafin ƙuna. 17 Gama Ɗan Ragon da yake a tsakiyar kursiyin zai zama makiyayinsu;‘zai bi da su zuwa ga maɓulɓular ruwan rai.’‘Allah kuwa zai share dukan hawaye daga idanunsu.’ ”
In Other Versions
Revelation 7 in the ANGEFD
Revelation 7 in the ANTPNG2D
Revelation 7 in the AS21
Revelation 7 in the BAGH
Revelation 7 in the BBPNG
Revelation 7 in the BBT1E
Revelation 7 in the BDS
Revelation 7 in the BEV
Revelation 7 in the BHAD
Revelation 7 in the BIB
Revelation 7 in the BLPT
Revelation 7 in the BNT
Revelation 7 in the BNTABOOT
Revelation 7 in the BNTLV
Revelation 7 in the BOATCB
Revelation 7 in the BOATCB2
Revelation 7 in the BOBCV
Revelation 7 in the BOCNT
Revelation 7 in the BOECS
Revelation 7 in the BOGWICC
Revelation 7 in the BOHCV
Revelation 7 in the BOHLNT
Revelation 7 in the BOHNTLTAL
Revelation 7 in the BOICB
Revelation 7 in the BOILNTAP
Revelation 7 in the BOITCV
Revelation 7 in the BOKCV
Revelation 7 in the BOKCV2
Revelation 7 in the BOKHWOG
Revelation 7 in the BOKSSV
Revelation 7 in the BOLCB
Revelation 7 in the BOLCB2
Revelation 7 in the BOMCV
Revelation 7 in the BONAV
Revelation 7 in the BONCB
Revelation 7 in the BONLT
Revelation 7 in the BONUT2
Revelation 7 in the BOPLNT
Revelation 7 in the BOSCB
Revelation 7 in the BOSNC
Revelation 7 in the BOTLNT
Revelation 7 in the BOVCB
Revelation 7 in the BOYCB
Revelation 7 in the BPBB
Revelation 7 in the BPH
Revelation 7 in the BSB
Revelation 7 in the CCB
Revelation 7 in the CUV
Revelation 7 in the CUVS
Revelation 7 in the DBT
Revelation 7 in the DGDNT
Revelation 7 in the DHNT
Revelation 7 in the DNT
Revelation 7 in the ELBE
Revelation 7 in the EMTV
Revelation 7 in the ESV
Revelation 7 in the FBV
Revelation 7 in the FEB
Revelation 7 in the GGMNT
Revelation 7 in the GNT
Revelation 7 in the HARY
Revelation 7 in the HNT
Revelation 7 in the IRVA
Revelation 7 in the IRVB
Revelation 7 in the IRVG
Revelation 7 in the IRVH
Revelation 7 in the IRVK
Revelation 7 in the IRVM
Revelation 7 in the IRVM2
Revelation 7 in the IRVO
Revelation 7 in the IRVP
Revelation 7 in the IRVT
Revelation 7 in the IRVT2
Revelation 7 in the IRVU
Revelation 7 in the ISVN
Revelation 7 in the JSNT
Revelation 7 in the KAPI
Revelation 7 in the KBT1ETNIK
Revelation 7 in the KBV
Revelation 7 in the KJV
Revelation 7 in the KNFD
Revelation 7 in the LBA
Revelation 7 in the LBLA
Revelation 7 in the LNT
Revelation 7 in the LSV
Revelation 7 in the MAAL
Revelation 7 in the MBV
Revelation 7 in the MBV2
Revelation 7 in the MHNT
Revelation 7 in the MKNFD
Revelation 7 in the MNG
Revelation 7 in the MNT
Revelation 7 in the MNT2
Revelation 7 in the MRS1T
Revelation 7 in the NAA
Revelation 7 in the NASB
Revelation 7 in the NBLA
Revelation 7 in the NBS
Revelation 7 in the NBVTP
Revelation 7 in the NET2
Revelation 7 in the NIV11
Revelation 7 in the NNT
Revelation 7 in the NNT2
Revelation 7 in the NNT3
Revelation 7 in the PDDPT
Revelation 7 in the PFNT
Revelation 7 in the RMNT
Revelation 7 in the SBIAS
Revelation 7 in the SBIBS
Revelation 7 in the SBIBS2
Revelation 7 in the SBICS
Revelation 7 in the SBIDS
Revelation 7 in the SBIGS
Revelation 7 in the SBIHS
Revelation 7 in the SBIIS
Revelation 7 in the SBIIS2
Revelation 7 in the SBIIS3
Revelation 7 in the SBIKS
Revelation 7 in the SBIKS2
Revelation 7 in the SBIMS
Revelation 7 in the SBIOS
Revelation 7 in the SBIPS
Revelation 7 in the SBISS
Revelation 7 in the SBITS
Revelation 7 in the SBITS2
Revelation 7 in the SBITS3
Revelation 7 in the SBITS4
Revelation 7 in the SBIUS
Revelation 7 in the SBIVS
Revelation 7 in the SBT
Revelation 7 in the SBT1E
Revelation 7 in the SCHL
Revelation 7 in the SNT
Revelation 7 in the SUSU
Revelation 7 in the SUSU2
Revelation 7 in the SYNO
Revelation 7 in the TBIAOTANT
Revelation 7 in the TBT1E
Revelation 7 in the TBT1E2
Revelation 7 in the TFTIP
Revelation 7 in the TFTU
Revelation 7 in the TGNTATF3T
Revelation 7 in the THAI
Revelation 7 in the TNFD
Revelation 7 in the TNT
Revelation 7 in the TNTIK
Revelation 7 in the TNTIL
Revelation 7 in the TNTIN
Revelation 7 in the TNTIP
Revelation 7 in the TNTIZ
Revelation 7 in the TOMA
Revelation 7 in the TTENT
Revelation 7 in the UBG
Revelation 7 in the UGV
Revelation 7 in the UGV2
Revelation 7 in the UGV3
Revelation 7 in the VBL
Revelation 7 in the VDCC
Revelation 7 in the YALU
Revelation 7 in the YAPE
Revelation 7 in the YBVTP
Revelation 7 in the ZBP