Romans 11 (BOHCB)

1 To, ina da tambaya. Allah ya ƙi mutanensa ne? Sam, ko kaɗan! Ni mutumin Isra’ila ne kaina, zuriyar Ibrahim kuwa, daga kabilar Benyamin. 2 Allah bai ƙi mutanensa da ya rigya sani ba. Ba ku san abin da Nassi ya faɗa game da Iliya ba, yadda ya kawo kuka ga Allah a kan Isra’ila ya ce, 3 “Ya Ubangiji, sun karkashe annabawanka suka kuma rurrushe bagadanka; ni kaɗai na ragu, suna kuma neman raina”? 4 Wace amsa ce Allah ya ba shi? “Na keɓe wa kaina dubu bakwai waɗanda ba su yi wa Ba’al sujada ba.” 5 Haka ma, a wannan zamani akwai ragowar da aka zaɓa ta wurin alheri. 6 In kuwa na alheri ne, ba sauran cewa ya dogara ga ayyuka ke nan. In ba haka ba, ashe, alheri ba alheri ba ne kuma. 7 To, sai me? Abin da Isra’ila suka nema da himma ba su samu ba, amma zaɓaɓɓun suka samu. Sauran suka taurare, 8 kamar yadda yake a rubuce cewa,“Allah ya ba su ruhun ruɗewa,idanu don su kāsa gani,da kuma kunnuwa don su kāsa ji,har yă zuwa yau.” 9 Dawuda kuma ya ce,“Bari teburin cin abincinsu yă zama musu tarko,sanadin fāɗuwa da dutsen sa tuntuɓe da kuma ramuwa a kansu. 10 Bari idanunsu su duhunta don kada su iya gani,bayansu kuma yă tanƙware har abada.” 11 Har yanzu ina da tambaya. Sun yi tuntuɓe har ya kai ga fāɗuwar da ba za su iya tashi ba ne? Sam, ko kaɗan! A maimako, saboda laifinsu ne ceto ya zo ga Al’ummai don a sa mutanen Isra’ila su ji kishi. 12 Amma in laifinsu yana nufin albarka ga duniya, hasararsu kuma albarka ga Al’ummai, ina misalin yalwar da albarkunsu za su kawo! 13 Ina magana da ku ne fa Al’ummai. Tun da yake ni manzo ne ga Al’ummai, ina taƙama da aikin nan nawa, 14 da fata zan rura kabilata a ta kowace hanya su ji kishi har ma yă sa in ceci waɗansunsu. 15 Gama in ƙinsu da aka yi ya zama sulhu ga duniya, me karɓarsu za tă zama in ba rai daga matattu ba? 16 In sashen da aka miƙa a matsayin nunan fari tsattsarka ne, to, sauran ma tsattsarka ne; in saiwar tsattsarka ce, to, sauran rassan ma tsattsarka ne. 17 In an sassare waɗansu rassa, kai kuwa da kake kai zaitun jeji, aka ɗauke ka aka kuma yi muku aure, a yanzu kuwa kana shan ni’imar saiwar zaitun ɗin nan tare da sauran rassan, 18 kada ka yi taƙama cewa ka fi waɗancan rassan da aka sassare. In kuwa ka yi haka, to, ka yi la’akari da wannan. Ba kai ne kake taimakon saiwar ba, saiwar ce take taimakonka. 19 To, kana iya cewa, “An sassare rassan ne don a ɗaura aure da ni.” 20 Haka yake. Amma an sassare su ne saboda rashin bangaskiya, kai kuma kana tsaye ta wurin bangaskiya. Kada ka yi taƙama, sai dai ka ji tsoro. 21 Gama in har Allah bai bar rassan nan na asali ba, kai ma ba zai bar ka ba. 22 Ka lura fa da alheri da kuma tsananin Allah, tsanani ga waɗanda suka fāɗi, amma alheri a gare ka, da fata za ka ci gaba cikin alherinsa. In ba haka ba, kai ma za a sare ka. 23 In kuwa ba su nace cikin rashin bangaskiya ba, za a sāke ɗaura aure da su, domin Allah yana iya sāke haɗa su. 24 Kai ma da aka saro daga zaitun ɗin da asalinsa yake na jeji, aka ɗaura aure da kai a jikin zaitun ɗin na gida, saɓanin yadda aka saba, balle waɗannan rassa na asali, da za a ɗaura aure da su a jikin zaitun ɗin nan nasu na asali? 25 Ba na so ku kasance cikin rashin sani game da wannan asirin ’yan’uwa, domin kada ku ɗaga kai. Isra’ila sun ɗanɗana sashe na taurarewa har sai da shigowar Al’ummai masu yawa ya cika. 26 Ta haka kuwa za a ceci dukan Isra’ila, kamar yadda yake a rubuce cewa,“Mai ceto zai zo daga Sihiyona;zai kawar da rashin bin Allah daga Yaƙub. 27 Wannan kuwa shi ne alkawarina da susa’ad da na ɗauke musu zunubansu.” 28 Game da zancen nan na bishara kuwa, su abokan gāba ne saboda ku; amma game da zaɓen kuwa, su ƙaunatattunsa ne, albarkacin kakannin kakanninsu, 29 gama kyautar Allah da kiransa ba a sokewa. 30 Kamar yadda a dā can ku da kuke marasa biyayya ga Allah kuka sami jinƙai yanzu ta dalilin rashin biyayyarsu, 31 haka su ma suka zama marasa biyayya a yanzu domin su ma su sami jinƙai ta dalilin jinƙan da Allah ya yi muku. 32 Gama Allah ya daure dukan mutane ga rashin biyayya don yă nuna jinƙai ga kowa. 33 Kai, zurfin yalwar hikima da kuma sanin Allah yana nan a yalwace!Hukunce-hukuncensa kuma su fi gaban bincike,hanyoyinsa kuwa sun wuce gaban ganewa! 34 “Wa ya taɓa sanin zuciyar Ubangiji?Ko kuwa yă ba shi shawara?” 35 “Wa ya taɓa ba wa Allah wani abu,da Allah zai sāka masa?” 36 Gama daga gare shi, ta wurinsa, da kuma saboda shi ne dukan abubuwa suka kasance.Ɗaukaka ta tabbata a gare shi har abada! Amin.

In Other Versions

Romans 11 in the ANGEFD

Romans 11 in the ANTPNG2D

Romans 11 in the AS21

Romans 11 in the BAGH

Romans 11 in the BBPNG

Romans 11 in the BBT1E

Romans 11 in the BDS

Romans 11 in the BEV

Romans 11 in the BHAD

Romans 11 in the BIB

Romans 11 in the BLPT

Romans 11 in the BNT

Romans 11 in the BNTABOOT

Romans 11 in the BNTLV

Romans 11 in the BOATCB

Romans 11 in the BOATCB2

Romans 11 in the BOBCV

Romans 11 in the BOCNT

Romans 11 in the BOECS

Romans 11 in the BOGWICC

Romans 11 in the BOHCV

Romans 11 in the BOHLNT

Romans 11 in the BOHNTLTAL

Romans 11 in the BOICB

Romans 11 in the BOILNTAP

Romans 11 in the BOITCV

Romans 11 in the BOKCV

Romans 11 in the BOKCV2

Romans 11 in the BOKHWOG

Romans 11 in the BOKSSV

Romans 11 in the BOLCB

Romans 11 in the BOLCB2

Romans 11 in the BOMCV

Romans 11 in the BONAV

Romans 11 in the BONCB

Romans 11 in the BONLT

Romans 11 in the BONUT2

Romans 11 in the BOPLNT

Romans 11 in the BOSCB

Romans 11 in the BOSNC

Romans 11 in the BOTLNT

Romans 11 in the BOVCB

Romans 11 in the BOYCB

Romans 11 in the BPBB

Romans 11 in the BPH

Romans 11 in the BSB

Romans 11 in the CCB

Romans 11 in the CUV

Romans 11 in the CUVS

Romans 11 in the DBT

Romans 11 in the DGDNT

Romans 11 in the DHNT

Romans 11 in the DNT

Romans 11 in the ELBE

Romans 11 in the EMTV

Romans 11 in the ESV

Romans 11 in the FBV

Romans 11 in the FEB

Romans 11 in the GGMNT

Romans 11 in the GNT

Romans 11 in the HARY

Romans 11 in the HNT

Romans 11 in the IRVA

Romans 11 in the IRVB

Romans 11 in the IRVG

Romans 11 in the IRVH

Romans 11 in the IRVK

Romans 11 in the IRVM

Romans 11 in the IRVM2

Romans 11 in the IRVO

Romans 11 in the IRVP

Romans 11 in the IRVT

Romans 11 in the IRVT2

Romans 11 in the IRVU

Romans 11 in the ISVN

Romans 11 in the JSNT

Romans 11 in the KAPI

Romans 11 in the KBT1ETNIK

Romans 11 in the KBV

Romans 11 in the KJV

Romans 11 in the KNFD

Romans 11 in the LBA

Romans 11 in the LBLA

Romans 11 in the LNT

Romans 11 in the LSV

Romans 11 in the MAAL

Romans 11 in the MBV

Romans 11 in the MBV2

Romans 11 in the MHNT

Romans 11 in the MKNFD

Romans 11 in the MNG

Romans 11 in the MNT

Romans 11 in the MNT2

Romans 11 in the MRS1T

Romans 11 in the NAA

Romans 11 in the NASB

Romans 11 in the NBLA

Romans 11 in the NBS

Romans 11 in the NBVTP

Romans 11 in the NET2

Romans 11 in the NIV11

Romans 11 in the NNT

Romans 11 in the NNT2

Romans 11 in the NNT3

Romans 11 in the PDDPT

Romans 11 in the PFNT

Romans 11 in the RMNT

Romans 11 in the SBIAS

Romans 11 in the SBIBS

Romans 11 in the SBIBS2

Romans 11 in the SBICS

Romans 11 in the SBIDS

Romans 11 in the SBIGS

Romans 11 in the SBIHS

Romans 11 in the SBIIS

Romans 11 in the SBIIS2

Romans 11 in the SBIIS3

Romans 11 in the SBIKS

Romans 11 in the SBIKS2

Romans 11 in the SBIMS

Romans 11 in the SBIOS

Romans 11 in the SBIPS

Romans 11 in the SBISS

Romans 11 in the SBITS

Romans 11 in the SBITS2

Romans 11 in the SBITS3

Romans 11 in the SBITS4

Romans 11 in the SBIUS

Romans 11 in the SBIVS

Romans 11 in the SBT

Romans 11 in the SBT1E

Romans 11 in the SCHL

Romans 11 in the SNT

Romans 11 in the SUSU

Romans 11 in the SUSU2

Romans 11 in the SYNO

Romans 11 in the TBIAOTANT

Romans 11 in the TBT1E

Romans 11 in the TBT1E2

Romans 11 in the TFTIP

Romans 11 in the TFTU

Romans 11 in the TGNTATF3T

Romans 11 in the THAI

Romans 11 in the TNFD

Romans 11 in the TNT

Romans 11 in the TNTIK

Romans 11 in the TNTIL

Romans 11 in the TNTIN

Romans 11 in the TNTIP

Romans 11 in the TNTIZ

Romans 11 in the TOMA

Romans 11 in the TTENT

Romans 11 in the UBG

Romans 11 in the UGV

Romans 11 in the UGV2

Romans 11 in the UGV3

Romans 11 in the VBL

Romans 11 in the VDCC

Romans 11 in the YALU

Romans 11 in the YAPE

Romans 11 in the YBVTP

Romans 11 in the ZBP