Romans 6 (BOHCB)
1 Me za mu ce ke nan? Za mu ci gaba da yin zunubi domin alheri yă haɓaka? 2 Sam, ko kaɗan! Mun mutu ga zunubi; ta yaya za mu ci gaba da rayuwa a cikinsa kuma? 3 Ko ba ku sani ba cewa dukanmu da aka yi wa baftisma a cikin Kiristi Yesu an yi mana baftismar ne zuwa cikin mutuwarsa? 4 Saboda haka, an binne mu da shi ke nan, ta wurin baftisma cikin mutuwarsa, domin kamar yadda aka tā da Kiristi daga matattu ta wurin ɗaukakar Uba, haka mu ma mu yi zaman sabuwar rayuwa. 5 In kuwa mun zama ɗaya tare da shi haka a cikin mutuwarsa, tabbatacce mu ma za mu zama ɗaya tare da shi cikin tashinsa daga matattu. 6 Gama mun san cewa an gicciye halayenmu na dā tare da shi domin a kawar da jikin nan mai zunubi don kada mu ƙara zama bayi ga zunubi 7 domin duk wanda ya mutu an ’yantar da shi daga zunubi ke nan. 8 To, in mun mutu tare da Kiristi, mun gaskata cewa za mu rayu tare da shi kuma. 9 Gama mun san cewa da yake an tā da Kiristi daga matattu, ba zai sāke mutuwa ba; mutuwa ba ta da sauran iko a kansa. 10 Mutuwar da ya yi, ya mutu ne sau ɗaya tak, saboda yă shafe zunubi, amma rayuwar da yake yi, yana yi ne cikin tarayya da Allah. 11 Haka ku ma, ku ɗauke kanku matattu ne ga ikon zunubi amma rayayyu cikin tarayya da Allah cikin Kiristi Yesu. 12 Saboda haka kada ku bar zunubi yă mallaki jikin nan naku mai mutuwa yă sa ku zama masu biyayya ga mugayen sha’awace-sha’awacensa. 13 Kada ku miƙa gaɓoɓin jikinku ga zunubi a matsayin kayan aikin mugunta, sai dai ku miƙa kanku ga Allah, a matsayin waɗanda aka fitar da su daga mutuwa zuwa rai; ku kuma miƙa gaɓoɓin jikinku gare shi a matsayin kayan aikin adalci. 14 Gama zunubi ba zai zama maigidanku ba, domin ba kwa ƙarƙashin doka, sai dai ƙarƙashin alheri. 15 Me za mu ce ke nan? Za mu ci gaba yin zunubi domin ba ma ƙarƙashin doka sai dai ƙarƙashin alheri? Sam, ko kaɗan! 16 Ba ku sani ba cewa sa’ad da kuka miƙa kanku ga wani don ku yi masa biyayya a matsayin bayi, ko ku bayi ne ga zunubi, wanda yake kai ga mutuwa, ko kuwa ga biyayya, wadda take kai ga adalci, ashe, ba kun zama bayi ga wannan da kuke yi wa biyayya ba ke nan? 17 Amma godiya ga Allah don ko da yake a dā ku bayi ne ga ikon zunubi, da dukan zuciyarku kun yi biyayya ga irin koyarwar da aka danƙa muku. 18 An ’yanta ku daga zunubi, kun kuma zama bayi ga aikin adalci. 19 Ina magana ne kamar mutane saboda kun raunana a jikinku. Kamar yadda kuka saba miƙa gaɓoɓin jikinku a bautar abubuwan ƙazanta da mugun aiki a kan mugun aiki, saboda haka yanzu sai ku miƙa su bayi ga aikin adalci mai kai ga zaman tsarki. 20 Sa’ad da kuke bayin zunubi, ba ruwanku da aikin adalci. 21 Wace riba ce kuka samu a lokacin, daga abubuwan nan da yanzu suka zama muku abin kunya? Ƙarshen irin abubuwan nan dai, mutuwa ne! 22 Amma a yanzu da aka ’yantar da ku daga zunubi kuka kuma zama bayi ga Allah, ribar da kuka samu tana kai ga zaman tsarki, ƙarshenta kuwa rai madawwami ne. 23 Gama sakamakon zunubi mutuwa ne, amma kyautar Allah rai madawwami ne a cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.
In Other Versions
Romans 6 in the ANGEFD
Romans 6 in the ANTPNG2D
Romans 6 in the AS21
Romans 6 in the BAGH
Romans 6 in the BBPNG
Romans 6 in the BBT1E
Romans 6 in the BDS
Romans 6 in the BEV
Romans 6 in the BHAD
Romans 6 in the BIB
Romans 6 in the BLPT
Romans 6 in the BNT
Romans 6 in the BNTABOOT
Romans 6 in the BNTLV
Romans 6 in the BOATCB
Romans 6 in the BOATCB2
Romans 6 in the BOBCV
Romans 6 in the BOCNT
Romans 6 in the BOECS
Romans 6 in the BOGWICC
Romans 6 in the BOHCV
Romans 6 in the BOHLNT
Romans 6 in the BOHNTLTAL
Romans 6 in the BOICB
Romans 6 in the BOILNTAP
Romans 6 in the BOITCV
Romans 6 in the BOKCV
Romans 6 in the BOKCV2
Romans 6 in the BOKHWOG
Romans 6 in the BOKSSV
Romans 6 in the BOLCB
Romans 6 in the BOLCB2
Romans 6 in the BOMCV
Romans 6 in the BONAV
Romans 6 in the BONCB
Romans 6 in the BONLT
Romans 6 in the BONUT2
Romans 6 in the BOPLNT
Romans 6 in the BOSCB
Romans 6 in the BOSNC
Romans 6 in the BOTLNT
Romans 6 in the BOVCB
Romans 6 in the BOYCB
Romans 6 in the BPBB
Romans 6 in the BPH
Romans 6 in the BSB
Romans 6 in the CCB
Romans 6 in the CUV
Romans 6 in the CUVS
Romans 6 in the DBT
Romans 6 in the DGDNT
Romans 6 in the DHNT
Romans 6 in the DNT
Romans 6 in the ELBE
Romans 6 in the EMTV
Romans 6 in the ESV
Romans 6 in the FBV
Romans 6 in the FEB
Romans 6 in the GGMNT
Romans 6 in the GNT
Romans 6 in the HARY
Romans 6 in the HNT
Romans 6 in the IRVA
Romans 6 in the IRVB
Romans 6 in the IRVG
Romans 6 in the IRVH
Romans 6 in the IRVK
Romans 6 in the IRVM
Romans 6 in the IRVM2
Romans 6 in the IRVO
Romans 6 in the IRVP
Romans 6 in the IRVT
Romans 6 in the IRVT2
Romans 6 in the IRVU
Romans 6 in the ISVN
Romans 6 in the JSNT
Romans 6 in the KAPI
Romans 6 in the KBT1ETNIK
Romans 6 in the KBV
Romans 6 in the KJV
Romans 6 in the KNFD
Romans 6 in the LBA
Romans 6 in the LBLA
Romans 6 in the LNT
Romans 6 in the LSV
Romans 6 in the MAAL
Romans 6 in the MBV
Romans 6 in the MBV2
Romans 6 in the MHNT
Romans 6 in the MKNFD
Romans 6 in the MNG
Romans 6 in the MNT
Romans 6 in the MNT2
Romans 6 in the MRS1T
Romans 6 in the NAA
Romans 6 in the NASB
Romans 6 in the NBLA
Romans 6 in the NBS
Romans 6 in the NBVTP
Romans 6 in the NET2
Romans 6 in the NIV11
Romans 6 in the NNT
Romans 6 in the NNT2
Romans 6 in the NNT3
Romans 6 in the PDDPT
Romans 6 in the PFNT
Romans 6 in the RMNT
Romans 6 in the SBIAS
Romans 6 in the SBIBS
Romans 6 in the SBIBS2
Romans 6 in the SBICS
Romans 6 in the SBIDS
Romans 6 in the SBIGS
Romans 6 in the SBIHS
Romans 6 in the SBIIS
Romans 6 in the SBIIS2
Romans 6 in the SBIIS3
Romans 6 in the SBIKS
Romans 6 in the SBIKS2
Romans 6 in the SBIMS
Romans 6 in the SBIOS
Romans 6 in the SBIPS
Romans 6 in the SBISS
Romans 6 in the SBITS
Romans 6 in the SBITS2
Romans 6 in the SBITS3
Romans 6 in the SBITS4
Romans 6 in the SBIUS
Romans 6 in the SBIVS
Romans 6 in the SBT
Romans 6 in the SBT1E
Romans 6 in the SCHL
Romans 6 in the SNT
Romans 6 in the SUSU
Romans 6 in the SUSU2
Romans 6 in the SYNO
Romans 6 in the TBIAOTANT
Romans 6 in the TBT1E
Romans 6 in the TBT1E2
Romans 6 in the TFTIP
Romans 6 in the TFTU
Romans 6 in the TGNTATF3T
Romans 6 in the THAI
Romans 6 in the TNFD
Romans 6 in the TNT
Romans 6 in the TNTIK
Romans 6 in the TNTIL
Romans 6 in the TNTIN
Romans 6 in the TNTIP
Romans 6 in the TNTIZ
Romans 6 in the TOMA
Romans 6 in the TTENT
Romans 6 in the UBG
Romans 6 in the UGV
Romans 6 in the UGV2
Romans 6 in the UGV3
Romans 6 in the VBL
Romans 6 in the VDCC
Romans 6 in the YALU
Romans 6 in the YAPE
Romans 6 in the YBVTP
Romans 6 in the ZBP