Luke 23 (BOHCB)

1 Sai dukan majalisa suka tashi, suka kai shi gaban Bilatus. 2 Suka fara zarginsa suna cewa, “Mun sami wannan mutum yana rikitar da al’ummarmu. Yana hana a biya haraji ga Kaisar. Yana kuma cewa, shi Kiristi ne, sarki kuma.” 3 Sai Bilatus ya tambayi Yesu ya ce, “Kai ne sarkin Yahudawa?”Yesu ya amsa ya ce, “I, haka yake, kamar yadda ka faɗa.” 4 Sai Bilatus ya sanar wa manyan firistoci da taron ya ce, “Ni fa, ban sami wani ainihin abin zargi game wannan mutum nan ba.” 5 Amma suka nace, suna cewa, “Yana tā da hankulan mutane, ko’ina a Yahudiya da koyarwarsa. Ya fara daga Galili, ga shi har ya kai nan.” 6 Da Bilatus ya ji haka, sai ya yi tambaya, “Ko shi mutumin Galili ne?” 7 Da ya ji cewa, Yesu yana ƙarƙashin mulkin Hiridus ne, sai ya aika da shi zuwa wurin Hiridus, don a lokacin Hiridus yana Urushalima. 8 Da Hiridus ya ga Yesu, sai ya yi murna ƙwarai, don tun dā ma yana marmari ya gan shi a kan abin da ya ji game da shi. Ya yi fata ya ga Yesu, yă kuma yi waɗansu ayyukan banmamaki. 9 Ya yi masa tambayoyi masu yawa, amma Yesu bai ba shi ko amsa ba. 10 Manyan firistoci da malaman dokoki suna tsaye a wurin, suna kawo zargi masu ƙarfi a kansa. 11 Sai Hiridus da sojojinsa suka wulaƙanta shi, suka yi masa ba’a. Sa’an nan, suka sa masa babban riga, suka mai da shi wurin Bilatus. 12 A ranar, Hiridus da Bilatus suka zama abokan juna, don tun dā ma, su abokan gāba ne. 13 Bilatus ya tara manyan firistoci, da masu mulki, da mutane, 14 ya ce musu, “Kun kawo mini wannan mutum, a matsayin wanda yana zuga mutane su yi tawaye. Na bincike shi a gabanku, ban ga a kan me kuka kawo kararsa ba. 15 Haka ma Hiridus, shi ya sa ya dawo da shi nan wurinmu. Kamar yadda ku ma kun gani, ba abin da mutumin nan ya yi, da ya isa mutuwa. 16 Saboda haka, zan yi masa bulala, in sāke shi.” 18 Suka yi ihu gaba ɗaya suka ce, “A yi gaba da wannan mutum! A sake mana Barabbas!” 19 (Barabbas yana kurkuku saboda laifin tā da hankali a birnin, da kuma don kisankai.) 20 Sai Bilatus ya sāke yin musu magana don yana so ya saki Yesu. 21 Amma sai suka ci gaba da ihu, suna cewa, “A gicciye shi! A gicciye shi!” 22 Ya sāke ce musu, sau na uku, “Don me? Wane laifi wannan mutum ya yi? Ni dai ban same shi da wani dalilin da ya isa a kashe shi ba. Saboda haka, zan sa a hore shi, sa’an nan in sāke shi.” 23 Amma suna ihu, suna nacewa, suna cewa, dole a gicciye shi, har ihunsu ya rinjaye shi. 24 Sai Bilatus ya biya bukatarsu da ya ji roƙonsu. 25 Ya saki mutumin da aka jefa a kurkuku saboda tā da hankali, da kisankai, shi wanda suka roƙa. Sa’an nan ya ba da Yesu ga nufinsu. 26 Sa’ad da suna tafiya da Yesu, sai wani da ake kira Siman, mutumin Sairin, yana zuwa daga ƙauye. Suka kama shi, suka aza masa gicciyen, suka tilasta shi ya ɗauki gicciyen, ya bi Yesu a baya. 27 Mutane da yawa sosai suka bi shi, a cikinsu ma da mata waɗanda suka yi makoki da kuka dominsa. 28 Yesu ya juya, ya ce musu, “’Yan matan Urushalima, kada ku yi kuka saboda ni, amma ku yi kuka saboda kanku, da kuma saboda ’ya’yanku. 29 Gama lokaci yana zuwa da za ku ce, ‘Masu albarka ne bakararru, wato, mata marasa haihuwa, da mahaihuwar da ba su taɓa haihuwa ba, da kuma mama da ba su taɓa shayar da nono ba!’ 30 Sa’an nan “ ‘za su ce wa duwatsu, “Ku fāɗi a kanmu!” Za su ce wa tuddai kuma, “Ku rufe mu!” ’ 31 Gama in mutane suna yin waɗannan abubuwa a lokacin da itace na ɗanye, me zai faru in ya bushe?” 32 Tare da shi akwai mutum biyu masu laifi, da aka tafi da su don a gicciye. 33 Da suka isa wurin da ake kira “Ƙoƙon Kai,” nan suka gicciye shi, tare da masu laifin nan, ɗaya a hannun damansa, ɗayan kuma a hagunsa. 34 Yesu ya ce, “Ya Uba ka yi musu gafara, don ba su san abin da suke yi ba.” Suka rarraba tufafinsa ta wurin jefa ƙuri’a. 35 Mutanen suka tsaya suna kallo. Har masu mulki ma suka yi masa ba’a, suna cewa, “Ya ceci waɗansu, to, ya ceci kansa in shi ne Kiristi na Allah, Zaɓaɓɓe.” 36 Sojoji su ma, suka zo suka yi masa ba’a. Suka miƙa masa ruwan tsami. 37 Suka ce, “In kai ne sarkin Yahudawa, ka ceci kanka mana.” 38 Bisa da shi kuma akwai rubutun da ya ce,Wannan shi ne Sarkin Yahudawa. 39 Ɗaya daga cikin masu laifin da aka gicciye a wurin ya zazzage shi ya ce, “Shin, ba kai ne Kiristi ba? To, ka ceci kanka, ka kuma cece mu mana!” 40 Amma ɗayan mai laifi ya kwaɓe shi ya ce, “Ba ka da tsoron Allah ne, wai saboda kana ƙarƙashin hukunci ɗaya tare da shi? 41 Horonmu, daidai aka yi mana, sakamakon abin da muka yi ne. Amma wannan mutum, bai yi wani laifi ba.” 42 Sai ya ce, “Yesu, ka tuna da ni sa’ad da ka shiga mulkinka.” 43 Yesu ya amsa, ya ce masa, “Gaskiya nake faɗa maka, yau ɗin nan, za ka kasance tare da ni, a mulkina a sama.” 44 Yanzu kuwa wajen sa’a ta shida ne, kuma duhu ya rufe ko’ina a ƙasar, har zuwa sa’a ta tara, 45 domin rana ta daina haskakawa. Labulen da yake cikin haikali kuma ya yage kashi biyu. 46 Yesu ya yi kira da babbar murya ya ce, “Ya Uba, na danƙa ruhuna a hannunka.” Da ya faɗi haka, sai ya ja numfashi na ƙarshe. 47 Da jarumin ya ga abin da ya faru, sai ya yabi Allah ya ce, “Gaskiya, wannan mutum mai adalci ne.” 48 Da dukan mutanen da suka taru, domin shaidar waɗannan abubuwa, suka ga abin da ya faru, sai suka buga ƙirjinsu suka tafi. 49 Amma dukan mutanen da suka san Yesu, tare da mata da suka bi shi daga Galili, suka tsaya daga nesa suna kallon abubuwan nan. 50 Akwai wani mutum mai suna Yusuf, ɗan Majalisa, wanda shi nagari ne, mai adalci, 51 shi dā ma bai yarda da shawararsu, da kuma abin da suka yi ba. Shi daga Arimateya ne wani garin Yahudiya. Yana kuma jiran zuwa mulkin Allah. 52 Sai ya je wurin Bilatus ya roƙa a ba shi jikin Yesu. 53 Sai ya saukar da jikin, ya nannaɗe shi a cikin zanen lilin, ya sa shi a wani kabari da aka fafe a cikin dutse, wadda ba a taɓa sa kowa ba. 54 An yi haka ne a Ranar Shirye-shirye, ranar Asabbaci kuma yana dab da farawa. 55 Matan da suka zo tare da Yesu, daga Galili suka bi Yusuf suka ga kabarin, da kuma yadda aka ajiye jikin. 56 Sa’an nan, suka koma gida, suka shirya kayan ƙanshi da turare. Amma suka huta a ranar Asabbaci don kiyaye doka.

In Other Versions

Luke 23 in the ANGEFD

Luke 23 in the ANTPNG2D

Luke 23 in the AS21

Luke 23 in the BAGH

Luke 23 in the BBPNG

Luke 23 in the BBT1E

Luke 23 in the BDS

Luke 23 in the BEV

Luke 23 in the BHAD

Luke 23 in the BIB

Luke 23 in the BLPT

Luke 23 in the BNT

Luke 23 in the BNTABOOT

Luke 23 in the BNTLV

Luke 23 in the BOATCB

Luke 23 in the BOATCB2

Luke 23 in the BOBCV

Luke 23 in the BOCNT

Luke 23 in the BOECS

Luke 23 in the BOGWICC

Luke 23 in the BOHCV

Luke 23 in the BOHLNT

Luke 23 in the BOHNTLTAL

Luke 23 in the BOICB

Luke 23 in the BOILNTAP

Luke 23 in the BOITCV

Luke 23 in the BOKCV

Luke 23 in the BOKCV2

Luke 23 in the BOKHWOG

Luke 23 in the BOKSSV

Luke 23 in the BOLCB

Luke 23 in the BOLCB2

Luke 23 in the BOMCV

Luke 23 in the BONAV

Luke 23 in the BONCB

Luke 23 in the BONLT

Luke 23 in the BONUT2

Luke 23 in the BOPLNT

Luke 23 in the BOSCB

Luke 23 in the BOSNC

Luke 23 in the BOTLNT

Luke 23 in the BOVCB

Luke 23 in the BOYCB

Luke 23 in the BPBB

Luke 23 in the BPH

Luke 23 in the BSB

Luke 23 in the CCB

Luke 23 in the CUV

Luke 23 in the CUVS

Luke 23 in the DBT

Luke 23 in the DGDNT

Luke 23 in the DHNT

Luke 23 in the DNT

Luke 23 in the ELBE

Luke 23 in the EMTV

Luke 23 in the ESV

Luke 23 in the FBV

Luke 23 in the FEB

Luke 23 in the GGMNT

Luke 23 in the GNT

Luke 23 in the HARY

Luke 23 in the HNT

Luke 23 in the IRVA

Luke 23 in the IRVB

Luke 23 in the IRVG

Luke 23 in the IRVH

Luke 23 in the IRVK

Luke 23 in the IRVM

Luke 23 in the IRVM2

Luke 23 in the IRVO

Luke 23 in the IRVP

Luke 23 in the IRVT

Luke 23 in the IRVT2

Luke 23 in the IRVU

Luke 23 in the ISVN

Luke 23 in the JSNT

Luke 23 in the KAPI

Luke 23 in the KBT1ETNIK

Luke 23 in the KBV

Luke 23 in the KJV

Luke 23 in the KNFD

Luke 23 in the LBA

Luke 23 in the LBLA

Luke 23 in the LNT

Luke 23 in the LSV

Luke 23 in the MAAL

Luke 23 in the MBV

Luke 23 in the MBV2

Luke 23 in the MHNT

Luke 23 in the MKNFD

Luke 23 in the MNG

Luke 23 in the MNT

Luke 23 in the MNT2

Luke 23 in the MRS1T

Luke 23 in the NAA

Luke 23 in the NASB

Luke 23 in the NBLA

Luke 23 in the NBS

Luke 23 in the NBVTP

Luke 23 in the NET2

Luke 23 in the NIV11

Luke 23 in the NNT

Luke 23 in the NNT2

Luke 23 in the NNT3

Luke 23 in the PDDPT

Luke 23 in the PFNT

Luke 23 in the RMNT

Luke 23 in the SBIAS

Luke 23 in the SBIBS

Luke 23 in the SBIBS2

Luke 23 in the SBICS

Luke 23 in the SBIDS

Luke 23 in the SBIGS

Luke 23 in the SBIHS

Luke 23 in the SBIIS

Luke 23 in the SBIIS2

Luke 23 in the SBIIS3

Luke 23 in the SBIKS

Luke 23 in the SBIKS2

Luke 23 in the SBIMS

Luke 23 in the SBIOS

Luke 23 in the SBIPS

Luke 23 in the SBISS

Luke 23 in the SBITS

Luke 23 in the SBITS2

Luke 23 in the SBITS3

Luke 23 in the SBITS4

Luke 23 in the SBIUS

Luke 23 in the SBIVS

Luke 23 in the SBT

Luke 23 in the SBT1E

Luke 23 in the SCHL

Luke 23 in the SNT

Luke 23 in the SUSU

Luke 23 in the SUSU2

Luke 23 in the SYNO

Luke 23 in the TBIAOTANT

Luke 23 in the TBT1E

Luke 23 in the TBT1E2

Luke 23 in the TFTIP

Luke 23 in the TFTU

Luke 23 in the TGNTATF3T

Luke 23 in the THAI

Luke 23 in the TNFD

Luke 23 in the TNT

Luke 23 in the TNTIK

Luke 23 in the TNTIL

Luke 23 in the TNTIN

Luke 23 in the TNTIP

Luke 23 in the TNTIZ

Luke 23 in the TOMA

Luke 23 in the TTENT

Luke 23 in the UBG

Luke 23 in the UGV

Luke 23 in the UGV2

Luke 23 in the UGV3

Luke 23 in the VBL

Luke 23 in the VDCC

Luke 23 in the YALU

Luke 23 in the YAPE

Luke 23 in the YBVTP

Luke 23 in the ZBP