Mark 12 (BOHCB)

1 Sa’an nan ya fara yi musu magana da misalai ya ce, “Wani mutum ya shuka gonar inabi. Ya kewaye ta da katanga, ya haƙa rami domin matsin inabin, ya kuma gina ɗakin gadi. Sai ya ba wa waɗansu manoma hayar gonar inabin, sa’an nan ya yi tafiya. 2 Da lokacin girbi ya yi, sai ya aiki wani bawa wajen ’yan hayan, don yă karɓo masa ’ya’yan inabin daga wurinsu. 3 Amma suka kama shi, suka yi masa dūka, suka kore shi hannun wofi. 4 Sai ya sāke aikan wani bawa wurinsu, amma suka bugi wannan mutum a kai, suka wulaƙanta shi. 5 Har yanzu ya sāke aikan wani. Wannan kuwa suka kashe. Ya aika waɗansu da yawa; suka bubbuge waɗansu, sauran kuwa suka kashe. 6 “Sauran mutum ɗaya da ya rage ya aika, ɗa, da yake ƙauna. Daga ƙarshe sai ya aike shi, yana cewa, ‘Za su girmama ɗana.’ 7 “Amma ’yan hayan suka ce wa juna, ‘Aha! Wannan shi ne magājin. Ku zo mu kashe shi, gādon kuma yă zama namu.’ 8 Sai suka kama shi suka kashe, suka jefa shi bayan gonar inabin. 9 “To, me, mai gonar inabin zai yi ke nan? Zai zo yă karkashe dukan ’yan hayan nan, ya kuma ba wa waɗansu gonar inabin. 10 Ba ku taɓa karanta wannan Nassi ba, “ ‘Dutsen da magina suka ƙi, shi ne kuwa ya zama dutsen kusurwan gini. 11 Ubangiji ya yi wannan, ya kuma yi kyau a idanunmu’?” 12 Sai manyan Firistoci da malaman dokoki da shugabanni suka nemi hanyar da za su kama shi, domin sun gane ya yi misalin a kansu ne. Amma suka ji tsoron taron, saboda haka suka bar shi suka yi tafiyarsu. 13 Daga baya, sai suka tura waɗansu Farisiyawa da mutanen Hiridus zuwa wurin Yesu, domin su sa masa tarko a cikin maganarsa. 14 Suka zo wurinsa suka ce, “Malam, mun san kai mutum ne mai mutunci. Ba ka bin ra’ayin mutane, don ba ka nuna bambanci. Amma kana koyar da hanyar Allah bisa ga gaskiya. Daidai ne a biya wa Kaisar haraji, ko babu? 15 Mu biya ko kada mu biya?”Amma Yesu ya san munafuncinsu, sai ya yi tambaya ya ce, “Don me kuke ƙoƙarin sa mini tarko? Ku kawo mini dinari in ga.” 16 Suka kawo masa kuɗin, sai ya tambaye, su ya ce, “Hoton wane ne wannan? Kuma rubutun wane ne wannan?”Suka ce, “Na Kaisar.” 17 Sai Yesu ya ce musu, “Ku ba wa Kaisar abin da yake na Kaisar, ku ba wa Allah kuma abin da yake na Allah.”Suka yi mamakinsa ƙwarai. 18 Sa’an nan Sadukiyawa da suke cewa, babu tashin matattu, suka zo masa da tambaya. 19 Suka ce, “Malam, Musa ya rubuta mana cewa, in ɗan’uwan wani mutum ya mutu, ya bar mata babu ’ya’ya, dole mutumin ya auri gwauruwar, yă kuma samo wa ɗan’uwansa ’ya’ya. 20 To, an yi waɗansu ’yan’uwa guda bakwai. Na fari ya yi aure, ya mutu babu ’ya’ya. 21 Na biyun ya auri gwauruwar, sai shi ma ya mutu, babu ’ya’ya. Haka kuma na ukun. 22 A gaskiya, ba ko ɗaya daga cikin bakwai ɗin da ya bar ’ya’ya. Daga ƙarshe, macen ta mutu. 23 To, a tashin matattu, matar wa za tă zama, don duk su bakwai nan sun aure ta?” 24 Yesu ya ce, “Ashe, ba a cikin kuskure kuke ba saboda rashin sanin Nassi, ko ikon Allah? 25 Sa’ad da matattu suka tashi, ba za su yi aure ba, ba kuwa za a ba da su ga aure ba. Za su zama kamar yadda mala’iku suke a cikin sama. 26 Game da tashin matattu kuwa, ashe, ba ku karanta a cikin littafin Musa ba, game da labarin ɗan kurmin nan mai cin wuta da Musa ya gani a jeji, yadda Allah ya yi magana da shi ya ce, ‘Ni ne Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku da kuma Allah na Yaƙub’? 27 Shi ba Allah na matattu ba ne, shi Allah na masu rai ne. Kun yi mummunan kuskure!” 28 Wani daga cikin malaman dokoki ya zo ya ji suna muhawwara. Da ya lura cewa Yesu ya amsa musu daidai, sai ya tambaye shi ya ce, “A cikin dukan dokoki, wacce ta fi girma duka?” 29 Yesu ya ce, “Wadda ta fi girma duka, ita ce wannan. ‘Ku saurara, ya Isra’ila, Ubangiji Allahnmu, Ubangiji ɗaya ne. 30 Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan hankalinka, da kuma dukan ƙarfinka.’ 31 Na biyun ita ce, ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’ Ba wata doka da ta fi waɗannan.” 32 Mutumin ya ce, “Malam, ka faɗi daidai. Daidai ne da ka ce, Allah ɗaya ne, babu kuma wani sai shi. 33 Nuna ƙauna ga Allah da dukan zuciyarka, da dukan ganewarka, da dukan ƙarfinka, da kuma nuna ƙauna ga maƙwabcinka kamar kanka, ya fi dukan hadayun ƙonawa da sadakoki.” 34 Da Yesu ya ga ya amsa da hikima, sai ya ce masa, “Ba ka da nisa da mulkin Allah.” Daga lokacin, ba wanda ya yi karambani yin masa wata tambaya. 35 Yayinda Yesu yake koyarwa a filin haikalin, sai ya yi tambaya ya ce, “Yaya malaman dokoki suke cewa Kiristi ɗan Dawuda ne? 36 Dawuda da kansa ya yi magana ta wurin Ruhu Mai Tsarki ya ce, “ ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina, “Zauna a hannun damana sai na sa abokan gābanka a ƙarƙashin sawunka.” ’ 37 Dawuda da kansa ya kira shi ‘Ubangiji.’ To, ta yaya zai zama ɗansa?”Taro mai yawa suka saurare shi da murna. 38 Sa’ad da Yesu yake koyarwa ya ce, “Ku lura da malaman dokoki. Sukan so yin tafiya a manyan riguna, a kuma dinga gaishe su a wuraren kasuwanci. 39 Sukan kuma nemi wuraren zama mafi daraja a majami’u, da kuma wuraren zaman manya a bukukkuwa. 40 Suna ƙwace gidajen gwauraye, kuma don nuna iyawa, sukan yi dogayen addu’o’i. Irin mutanen nan, za su sha hukunci mai tsanani sosai.” 41 Yesu ya zauna ɗaura da inda ake bayarwa, ya kuma dubi yadda taron suke sa kuɗinsu a cikin ɗakunan ajiya haikali. Masu arziki da yawa suka zuba kuɗaɗe masu yawa. 42 Amma wata matalauciya gwauruwa, ta zo ta saka anini biyu, da suka yi daidai da rabin kobo. 43 Yesu ya kira almajiransa wurinsa ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, abin da matalauciya gwauruwan nan ta zuba cikin ɗakunan ajiya nan ya fi na sauran dukan. 44 Dukansu sun bayar ne daga cikin arzikinsu; ita kuwa, daga cikin talaucinta, ta ba da kome, duk abin da take da shi na rayuwa.”

In Other Versions

Mark 12 in the ANGEFD

Mark 12 in the ANTPNG2D

Mark 12 in the AS21

Mark 12 in the BAGH

Mark 12 in the BBPNG

Mark 12 in the BBT1E

Mark 12 in the BDS

Mark 12 in the BEV

Mark 12 in the BHAD

Mark 12 in the BIB

Mark 12 in the BLPT

Mark 12 in the BNT

Mark 12 in the BNTABOOT

Mark 12 in the BNTLV

Mark 12 in the BOATCB

Mark 12 in the BOATCB2

Mark 12 in the BOBCV

Mark 12 in the BOCNT

Mark 12 in the BOECS

Mark 12 in the BOGWICC

Mark 12 in the BOHCV

Mark 12 in the BOHLNT

Mark 12 in the BOHNTLTAL

Mark 12 in the BOICB

Mark 12 in the BOILNTAP

Mark 12 in the BOITCV

Mark 12 in the BOKCV

Mark 12 in the BOKCV2

Mark 12 in the BOKHWOG

Mark 12 in the BOKSSV

Mark 12 in the BOLCB

Mark 12 in the BOLCB2

Mark 12 in the BOMCV

Mark 12 in the BONAV

Mark 12 in the BONCB

Mark 12 in the BONLT

Mark 12 in the BONUT2

Mark 12 in the BOPLNT

Mark 12 in the BOSCB

Mark 12 in the BOSNC

Mark 12 in the BOTLNT

Mark 12 in the BOVCB

Mark 12 in the BOYCB

Mark 12 in the BPBB

Mark 12 in the BPH

Mark 12 in the BSB

Mark 12 in the CCB

Mark 12 in the CUV

Mark 12 in the CUVS

Mark 12 in the DBT

Mark 12 in the DGDNT

Mark 12 in the DHNT

Mark 12 in the DNT

Mark 12 in the ELBE

Mark 12 in the EMTV

Mark 12 in the ESV

Mark 12 in the FBV

Mark 12 in the FEB

Mark 12 in the GGMNT

Mark 12 in the GNT

Mark 12 in the HARY

Mark 12 in the HNT

Mark 12 in the IRVA

Mark 12 in the IRVB

Mark 12 in the IRVG

Mark 12 in the IRVH

Mark 12 in the IRVK

Mark 12 in the IRVM

Mark 12 in the IRVM2

Mark 12 in the IRVO

Mark 12 in the IRVP

Mark 12 in the IRVT

Mark 12 in the IRVT2

Mark 12 in the IRVU

Mark 12 in the ISVN

Mark 12 in the JSNT

Mark 12 in the KAPI

Mark 12 in the KBT1ETNIK

Mark 12 in the KBV

Mark 12 in the KJV

Mark 12 in the KNFD

Mark 12 in the LBA

Mark 12 in the LBLA

Mark 12 in the LNT

Mark 12 in the LSV

Mark 12 in the MAAL

Mark 12 in the MBV

Mark 12 in the MBV2

Mark 12 in the MHNT

Mark 12 in the MKNFD

Mark 12 in the MNG

Mark 12 in the MNT

Mark 12 in the MNT2

Mark 12 in the MRS1T

Mark 12 in the NAA

Mark 12 in the NASB

Mark 12 in the NBLA

Mark 12 in the NBS

Mark 12 in the NBVTP

Mark 12 in the NET2

Mark 12 in the NIV11

Mark 12 in the NNT

Mark 12 in the NNT2

Mark 12 in the NNT3

Mark 12 in the PDDPT

Mark 12 in the PFNT

Mark 12 in the RMNT

Mark 12 in the SBIAS

Mark 12 in the SBIBS

Mark 12 in the SBIBS2

Mark 12 in the SBICS

Mark 12 in the SBIDS

Mark 12 in the SBIGS

Mark 12 in the SBIHS

Mark 12 in the SBIIS

Mark 12 in the SBIIS2

Mark 12 in the SBIIS3

Mark 12 in the SBIKS

Mark 12 in the SBIKS2

Mark 12 in the SBIMS

Mark 12 in the SBIOS

Mark 12 in the SBIPS

Mark 12 in the SBISS

Mark 12 in the SBITS

Mark 12 in the SBITS2

Mark 12 in the SBITS3

Mark 12 in the SBITS4

Mark 12 in the SBIUS

Mark 12 in the SBIVS

Mark 12 in the SBT

Mark 12 in the SBT1E

Mark 12 in the SCHL

Mark 12 in the SNT

Mark 12 in the SUSU

Mark 12 in the SUSU2

Mark 12 in the SYNO

Mark 12 in the TBIAOTANT

Mark 12 in the TBT1E

Mark 12 in the TBT1E2

Mark 12 in the TFTIP

Mark 12 in the TFTU

Mark 12 in the TGNTATF3T

Mark 12 in the THAI

Mark 12 in the TNFD

Mark 12 in the TNT

Mark 12 in the TNTIK

Mark 12 in the TNTIL

Mark 12 in the TNTIN

Mark 12 in the TNTIP

Mark 12 in the TNTIZ

Mark 12 in the TOMA

Mark 12 in the TTENT

Mark 12 in the UBG

Mark 12 in the UGV

Mark 12 in the UGV2

Mark 12 in the UGV3

Mark 12 in the VBL

Mark 12 in the VDCC

Mark 12 in the YALU

Mark 12 in the YAPE

Mark 12 in the YBVTP

Mark 12 in the ZBP