1 Peter 1 (BOHCB)

1 Bitrus, manzon Yesu Kiristi, Zuwa ga zaɓaɓɓu na Allah, baƙi a duniya, da suke a warwatse ko’ina a Fontus, Galatiya, Kaffadokiya, Asiya da kuma Bitiniya, 2 waɗanda aka zaɓa bisa ga rigyasanin Allah Uba, ta wurin aikin tsarkakewar Ruhu, don biyayya ga Yesu Kiristi, su kuma sami yayyafan jininsa. Alheri da salama su zama naku a yalwace. 3 Yabo ya tabbata ga Allah Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi! Cikin jinƙansa mai girma ya ba mu sabuwar haihuwa cikin bege mai rai ta wurin tashin Yesu Kiristi daga matattu, 4 da kuma cikin gādon da ba zai taɓa lalacewa, ɓacewa ko koɗewa ba, ajiyayye a sama dominku, 5 ku waɗanda ta wurin bangaskiya ake kiyayewa ta wurin ikon Allah har yă zuwa ceton da yake a shirye da za a bayyana a ƙarshen lokaci. 6 A kan wannan kuke cike da farin ciki ƙwarai, ko da yake yanzu na ɗan lokaci kuna fuskantar baƙin ciki daga gwaje-gwaje iri-iri. 7 Wannan kuwa domin a tabbatar da sahihancin bangaskiyarku ne, wadda ta fi zinariya daraja nesa, ita zinariya kuwa, ko da yake mai ƙarewa ce, akan gwada ta da wuta, domin bangaskiyan nan taku ta jawo muku yabo da girma da ɗaukaka a bayyanar Yesu Kiristi. 8 Ko da yake ba ku taɓa ganinsa ba, kuna ƙaunarsa; kuma ko da yake ba kwa ganinsa yanzu, kun gaskata shi, kun kuma cika da farin ciki ƙwarai, wanda ya fi gaban faɗi, 9 gama kuna samun sakamakon bangaskiyarku, ceton rayukanku ke nan. 10 Game da ceton nan, annabawa, waɗanda suka yi maganar alherin da za tă zo gare ku, sun yi bincike mai zurfi, a natse, 11 suna ƙoƙari su san lokaci da kuma yanayin da Ruhun Kiristi da yake cikinsu yana nunawa sa’ad da ya yi faɗi a kan wahalolin Kiristi da kuma ɗaukaka da za tă bi. 12 Aka bayyana musu cewa ba kansu ne suke bauta wa ba sai ku, sa’ad da suka yi maganar abubuwan da aka faɗa muku ta wurin waɗanda suka yi muku wa’azin bishara, ta wurin Ruhu Mai Tsarki wanda aka aika daga sama. Ko mala’iku ma suna marmari su ga waɗannan abubuwa. 13 Saboda haka, ku shirya kanku don aiki; ku zama masu kamunkai; ku kafa begenku duka a kan alherin da za a ba ku sa’ad da aka bayyana Yesu Kiristi. 14 Kamar ’ya’ya masu biyayya, kada ku bi mugayen sha’awace-sha’awacen da dā kuke da su sa’ad da kuke rayuwa a cikin jahilci. 15 Amma kamar yadda wanda ya kira ku yake mai tsarki, haka ku ma sai ku kasance masu tsarki cikin dukan abubuwan da kuke yi; 16 gama a rubuce yake cewa, “Ku zama masu tsarki, domin ni mai tsarki ne.” 17 Tun da yake kuna kira ga Uba wanda yake yin wa kowane mutum shari’a bisa ga ayyukansa ba bambanci, sai ku yi rayuwarku a nan kamar baƙi cikin tsoro mai bangirma. 18 Gama kun san cewa ba da abubuwa masu lalacewa kamar azurfa ko zinariya ce aka fanshe ku daga rayuwar banza da kuka karɓa daga kakanni-kakanninku ba, 19 sai dai an fanshe ku da jini mai daraja na Kiristi, ɗan rago marar aibi ko lahani. 20 An zaɓe shi kafin halittar duniya, amma an bayyana shi a zamanin ƙarshe saboda ku. 21 Ta gare shi ne kuka gaskata da Allah, wanda ya tā da shi daga matattu, aka kuma ɗaukaka shi, ta haka bari bangaskiyarku da begenku su kasance ga Allah. 22 Yanzu da kuka tsarkake kanku ta wurin yin biyayya ga gaskiyan nan, don ku kasance da ƙauna mai gaskiya wa ’yan’uwanku, sai ku ƙaunaci juna ƙwarai, daga zuciya. 23 Gama an sāke haihuwarku, ba da iri da yake lalacewa ba, sai dai marar lalacewa, ta wurin rayayyiya da kuma madawwamiyar maganar Allah. 24 Gama,“Dukan mutane kamar ciyawa suke,darajarsu kuma kamar furannin jeji ne;ciyawa takan yanƙwane furannin kuma su kakkaɓe, 25 amma maganar Ubangiji tana nan har abada.”Wannan kuwa ita ce kalmar da aka yi muku wa’azi.

In Other Versions

1 Peter 1 in the ANGEFD

1 Peter 1 in the ANTPNG2D

1 Peter 1 in the AS21

1 Peter 1 in the BAGH

1 Peter 1 in the BBPNG

1 Peter 1 in the BBT1E

1 Peter 1 in the BDS

1 Peter 1 in the BEV

1 Peter 1 in the BHAD

1 Peter 1 in the BIB

1 Peter 1 in the BLPT

1 Peter 1 in the BNT

1 Peter 1 in the BNTABOOT

1 Peter 1 in the BNTLV

1 Peter 1 in the BOATCB

1 Peter 1 in the BOATCB2

1 Peter 1 in the BOBCV

1 Peter 1 in the BOCNT

1 Peter 1 in the BOECS

1 Peter 1 in the BOGWICC

1 Peter 1 in the BOHCV

1 Peter 1 in the BOHLNT

1 Peter 1 in the BOHNTLTAL

1 Peter 1 in the BOICB

1 Peter 1 in the BOILNTAP

1 Peter 1 in the BOITCV

1 Peter 1 in the BOKCV

1 Peter 1 in the BOKCV2

1 Peter 1 in the BOKHWOG

1 Peter 1 in the BOKSSV

1 Peter 1 in the BOLCB

1 Peter 1 in the BOLCB2

1 Peter 1 in the BOMCV

1 Peter 1 in the BONAV

1 Peter 1 in the BONCB

1 Peter 1 in the BONLT

1 Peter 1 in the BONUT2

1 Peter 1 in the BOPLNT

1 Peter 1 in the BOSCB

1 Peter 1 in the BOSNC

1 Peter 1 in the BOTLNT

1 Peter 1 in the BOVCB

1 Peter 1 in the BOYCB

1 Peter 1 in the BPBB

1 Peter 1 in the BPH

1 Peter 1 in the BSB

1 Peter 1 in the CCB

1 Peter 1 in the CUV

1 Peter 1 in the CUVS

1 Peter 1 in the DBT

1 Peter 1 in the DGDNT

1 Peter 1 in the DHNT

1 Peter 1 in the DNT

1 Peter 1 in the ELBE

1 Peter 1 in the EMTV

1 Peter 1 in the ESV

1 Peter 1 in the FBV

1 Peter 1 in the FEB

1 Peter 1 in the GGMNT

1 Peter 1 in the GNT

1 Peter 1 in the HARY

1 Peter 1 in the HNT

1 Peter 1 in the IRVA

1 Peter 1 in the IRVB

1 Peter 1 in the IRVG

1 Peter 1 in the IRVH

1 Peter 1 in the IRVK

1 Peter 1 in the IRVM

1 Peter 1 in the IRVM2

1 Peter 1 in the IRVO

1 Peter 1 in the IRVP

1 Peter 1 in the IRVT

1 Peter 1 in the IRVT2

1 Peter 1 in the IRVU

1 Peter 1 in the ISVN

1 Peter 1 in the JSNT

1 Peter 1 in the KAPI

1 Peter 1 in the KBT1ETNIK

1 Peter 1 in the KBV

1 Peter 1 in the KJV

1 Peter 1 in the KNFD

1 Peter 1 in the LBA

1 Peter 1 in the LBLA

1 Peter 1 in the LNT

1 Peter 1 in the LSV

1 Peter 1 in the MAAL

1 Peter 1 in the MBV

1 Peter 1 in the MBV2

1 Peter 1 in the MHNT

1 Peter 1 in the MKNFD

1 Peter 1 in the MNG

1 Peter 1 in the MNT

1 Peter 1 in the MNT2

1 Peter 1 in the MRS1T

1 Peter 1 in the NAA

1 Peter 1 in the NASB

1 Peter 1 in the NBLA

1 Peter 1 in the NBS

1 Peter 1 in the NBVTP

1 Peter 1 in the NET2

1 Peter 1 in the NIV11

1 Peter 1 in the NNT

1 Peter 1 in the NNT2

1 Peter 1 in the NNT3

1 Peter 1 in the PDDPT

1 Peter 1 in the PFNT

1 Peter 1 in the RMNT

1 Peter 1 in the SBIAS

1 Peter 1 in the SBIBS

1 Peter 1 in the SBIBS2

1 Peter 1 in the SBICS

1 Peter 1 in the SBIDS

1 Peter 1 in the SBIGS

1 Peter 1 in the SBIHS

1 Peter 1 in the SBIIS

1 Peter 1 in the SBIIS2

1 Peter 1 in the SBIIS3

1 Peter 1 in the SBIKS

1 Peter 1 in the SBIKS2

1 Peter 1 in the SBIMS

1 Peter 1 in the SBIOS

1 Peter 1 in the SBIPS

1 Peter 1 in the SBISS

1 Peter 1 in the SBITS

1 Peter 1 in the SBITS2

1 Peter 1 in the SBITS3

1 Peter 1 in the SBITS4

1 Peter 1 in the SBIUS

1 Peter 1 in the SBIVS

1 Peter 1 in the SBT

1 Peter 1 in the SBT1E

1 Peter 1 in the SCHL

1 Peter 1 in the SNT

1 Peter 1 in the SUSU

1 Peter 1 in the SUSU2

1 Peter 1 in the SYNO

1 Peter 1 in the TBIAOTANT

1 Peter 1 in the TBT1E

1 Peter 1 in the TBT1E2

1 Peter 1 in the TFTIP

1 Peter 1 in the TFTU

1 Peter 1 in the TGNTATF3T

1 Peter 1 in the THAI

1 Peter 1 in the TNFD

1 Peter 1 in the TNT

1 Peter 1 in the TNTIK

1 Peter 1 in the TNTIL

1 Peter 1 in the TNTIN

1 Peter 1 in the TNTIP

1 Peter 1 in the TNTIZ

1 Peter 1 in the TOMA

1 Peter 1 in the TTENT

1 Peter 1 in the UBG

1 Peter 1 in the UGV

1 Peter 1 in the UGV2

1 Peter 1 in the UGV3

1 Peter 1 in the VBL

1 Peter 1 in the VDCC

1 Peter 1 in the YALU

1 Peter 1 in the YAPE

1 Peter 1 in the YBVTP

1 Peter 1 in the ZBP