Acts 1 (BOHCB)

1 A littafina na farko, Tiyofilus, na rubuta game da dukan abin da Yesu ya fara yi, da abin da ya koyar 2 har zuwa ranar da aka ɗauke shi zuwa sama, bayan ya ba da umarnai ta wurin Ruhu Mai Tsarki ga manzannin da ya zaɓa. 3 Bayan wahalarsa, ya bayyana kansa ga waɗannan mutane ya kuma ba da tabbatattun alamu masu yawa cewa yana da rai. Ya bayyana a gare su har kwana arba’in ya kuma yi musu magana game da mulkin Allah. 4 A wani lokaci, yayinda yake ci tare da su, ya ba su wannan umarni, “Kada ku bar Urushalima, amma ku jira kyautar da Ubana ya yi alkawari, wadda kuka ji na yi magana a kai. 5 Gama Yohanna ya yi baftisma da ruwa, amma a cikin ’yan kwanaki za a yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki.” 6 Saboda haka, sa’ad da suka taru, sai suka tambaye shi, “Ubangiji, a wannan lokaci za ka mayar da mulki ga Isra’ila?” 7 Ya ce musu, “Ba naku ba ne ku san lokuta ko ranakun da Uban ya shirya cikin ikonsa. 8 Amma ku za ku karɓi iko sa’ad da Ruhu Mai Tsarki ya sauka a kanku; za ku kuma zama shaiduna cikin Urushalima, da kuma cikin dukan Yahudiya da Samariya, zuwa kuma iyakar duniya.” 9 Bayan ya faɗi wannan, sai aka ɗauke shi sama a idanunsu sai wani girgije ya rufe shi daga ganinsu. 10 Suna zuba ido a bisa, zuwa cikin sararin sama yayinda yake tafiya, nan da nan, sai ga mutane biyu saye da fararen riguna tsaye kusa da su. 11 Sai suka ce, “Mutanen Galili, don me kuke tsaye a nan kuna duban sararin sama? Wannan Yesu, wanda aka ɗauke daga gare ku zuwa sama, zai komo daidai yadda kuka ga ya tafi sama.” 12 Sai suka koma Urushalima daga tudun da ake kira Dutsen Zaitun, tafiyar ranar Asabbaci guda daga birnin. 13 Da suka iso, sai suka hau gidan sama, zuwa ɗakin da suke zama. Waɗanda suka kasance kuwa su ne, Bitrus, Yohanna, Yaƙub da Andarawus;Filibus da Toma;Bartolomeyu da Mattiyu;Yaƙub ɗan Alfayus da Siman Zilot, da kuma Yahuda ɗan Yaƙub. 14 Waɗannan duka suka duƙufa cikin addu’a, tare da waɗansu mata da Maryamu mahaifiyar Yesu, da kuma tare da ’yan’uwansa. 15 A waɗancan kwanakin Bitrus ya miƙe tsaye cikin ’yan’uwa masu bi (taron da ya yi kusan mutum ɗari da ashirin) 16 ya ce, “’Yan’uwana, dole a cika Nassin nan da Ruhu Mai Tsarki ya yi magana tun da daɗewa ta bakin Dawuda game da Yahuda, wanda ya zama jagora ga waɗanda suka kama Yesu 17 dā shi ɗaya ne cikinmu, ya kuma yi hidima a cikin aikin nan.” 18 (Da ladar da ya samu saboda muguntarsa Yahuda ya sayi wani fili; a can ya fāɗi da kā, jikinsa ya fashe, hanjinsa kuma duk suka zubo. 19 Kowa a Urushalima ya ji game da wannan, saboda haka suka kira wannan filin Akeldama, da yarensu, wato, Filin Jini.) 20 Bitrus ya ce, “Gama yana a rubuce a cikin Littafin Zabura cewa,“ ‘Bari wurinsa yă zama babu kowa;kada kowa ya zauna a cikinsa,’kuma,“ ‘Bari wani ya ɗauki matsayinsa na shugabanci.’ 21 Saboda haka dole a zaɓi ɗaya daga cikin mutanen da suke tare da mu duk lokacin da Ubangiji Yesu yake shiga da fita a cikinmu, 22 farawa daga baftisma ta Yohanna har zuwa sa’ad da aka ɗauke Yesu daga gare mu. Gama dole ɗaya daga waɗannan ya zama shaidar tashinsa daga matattu tare da mu.” 23 Saboda haka suka gabatar da mutane biyu. Yusuf mai suna Barsabbas (da aka kuma sani da Yustus) da kuma Mattiyas. 24 Sai suka yi addu’a suka ce, “Ubangiji, ka san zuciyar kowa. Nuna mana wanne a cikin waɗannan biyu da ka zaɓa 25 ya karɓi wannan aikin manzanci, wanda Yahuda ya bari don yă tafi wurin da yake nasa.” 26 Sa’an nan suka jefa ƙuri’u, ƙuri’ar kuwa ta fāɗo a kan Mattiyas; sai aka sa shi cikin manzannin nan goma sha ɗaya.

In Other Versions

Acts 1 in the ANGEFD

Acts 1 in the ANTPNG2D

Acts 1 in the AS21

Acts 1 in the BAGH

Acts 1 in the BBPNG

Acts 1 in the BBT1E

Acts 1 in the BDS

Acts 1 in the BEV

Acts 1 in the BHAD

Acts 1 in the BIB

Acts 1 in the BLPT

Acts 1 in the BNT

Acts 1 in the BNTABOOT

Acts 1 in the BNTLV

Acts 1 in the BOATCB

Acts 1 in the BOATCB2

Acts 1 in the BOBCV

Acts 1 in the BOCNT

Acts 1 in the BOECS

Acts 1 in the BOGWICC

Acts 1 in the BOHCV

Acts 1 in the BOHLNT

Acts 1 in the BOHNTLTAL

Acts 1 in the BOICB

Acts 1 in the BOILNTAP

Acts 1 in the BOITCV

Acts 1 in the BOKCV

Acts 1 in the BOKCV2

Acts 1 in the BOKHWOG

Acts 1 in the BOKSSV

Acts 1 in the BOLCB

Acts 1 in the BOLCB2

Acts 1 in the BOMCV

Acts 1 in the BONAV

Acts 1 in the BONCB

Acts 1 in the BONLT

Acts 1 in the BONUT2

Acts 1 in the BOPLNT

Acts 1 in the BOSCB

Acts 1 in the BOSNC

Acts 1 in the BOTLNT

Acts 1 in the BOVCB

Acts 1 in the BOYCB

Acts 1 in the BPBB

Acts 1 in the BPH

Acts 1 in the BSB

Acts 1 in the CCB

Acts 1 in the CUV

Acts 1 in the CUVS

Acts 1 in the DBT

Acts 1 in the DGDNT

Acts 1 in the DHNT

Acts 1 in the DNT

Acts 1 in the ELBE

Acts 1 in the EMTV

Acts 1 in the ESV

Acts 1 in the FBV

Acts 1 in the FEB

Acts 1 in the GGMNT

Acts 1 in the GNT

Acts 1 in the HARY

Acts 1 in the HNT

Acts 1 in the IRVA

Acts 1 in the IRVB

Acts 1 in the IRVG

Acts 1 in the IRVH

Acts 1 in the IRVK

Acts 1 in the IRVM

Acts 1 in the IRVM2

Acts 1 in the IRVO

Acts 1 in the IRVP

Acts 1 in the IRVT

Acts 1 in the IRVT2

Acts 1 in the IRVU

Acts 1 in the ISVN

Acts 1 in the JSNT

Acts 1 in the KAPI

Acts 1 in the KBT1ETNIK

Acts 1 in the KBV

Acts 1 in the KJV

Acts 1 in the KNFD

Acts 1 in the LBA

Acts 1 in the LBLA

Acts 1 in the LNT

Acts 1 in the LSV

Acts 1 in the MAAL

Acts 1 in the MBV

Acts 1 in the MBV2

Acts 1 in the MHNT

Acts 1 in the MKNFD

Acts 1 in the MNG

Acts 1 in the MNT

Acts 1 in the MNT2

Acts 1 in the MRS1T

Acts 1 in the NAA

Acts 1 in the NASB

Acts 1 in the NBLA

Acts 1 in the NBS

Acts 1 in the NBVTP

Acts 1 in the NET2

Acts 1 in the NIV11

Acts 1 in the NNT

Acts 1 in the NNT2

Acts 1 in the NNT3

Acts 1 in the PDDPT

Acts 1 in the PFNT

Acts 1 in the RMNT

Acts 1 in the SBIAS

Acts 1 in the SBIBS

Acts 1 in the SBIBS2

Acts 1 in the SBICS

Acts 1 in the SBIDS

Acts 1 in the SBIGS

Acts 1 in the SBIHS

Acts 1 in the SBIIS

Acts 1 in the SBIIS2

Acts 1 in the SBIIS3

Acts 1 in the SBIKS

Acts 1 in the SBIKS2

Acts 1 in the SBIMS

Acts 1 in the SBIOS

Acts 1 in the SBIPS

Acts 1 in the SBISS

Acts 1 in the SBITS

Acts 1 in the SBITS2

Acts 1 in the SBITS3

Acts 1 in the SBITS4

Acts 1 in the SBIUS

Acts 1 in the SBIVS

Acts 1 in the SBT

Acts 1 in the SBT1E

Acts 1 in the SCHL

Acts 1 in the SNT

Acts 1 in the SUSU

Acts 1 in the SUSU2

Acts 1 in the SYNO

Acts 1 in the TBIAOTANT

Acts 1 in the TBT1E

Acts 1 in the TBT1E2

Acts 1 in the TFTIP

Acts 1 in the TFTU

Acts 1 in the TGNTATF3T

Acts 1 in the THAI

Acts 1 in the TNFD

Acts 1 in the TNT

Acts 1 in the TNTIK

Acts 1 in the TNTIL

Acts 1 in the TNTIN

Acts 1 in the TNTIP

Acts 1 in the TNTIZ

Acts 1 in the TOMA

Acts 1 in the TTENT

Acts 1 in the UBG

Acts 1 in the UGV

Acts 1 in the UGV2

Acts 1 in the UGV3

Acts 1 in the VBL

Acts 1 in the VDCC

Acts 1 in the YALU

Acts 1 in the YAPE

Acts 1 in the YBVTP

Acts 1 in the ZBP