John 11 (BOHCB)

1 To, an yi wani mutum mai suna Lazarus wanda ya yi rashin lafiya. Shi daga Betani ne, ƙauyen su Maryamu da ’yar’uwarta Marta. 2 Maryamun nan kuwa, wadda ɗan’uwanta Lazarus yake rashin lafiya, ita ce ta zuba wa Ubangiji turare ta kuma goge ƙafafunsa da gashin kanta. 3 Saboda haka ’yan’uwansa mata suka aika da saƙo wa Yesu cewa, “Ubangiji, wannan da kake ƙauna yana rashin lafiya.” 4 Sa’ad da ya ji haka, sai Yesu ya ce, “Wannan rashin lafiya ba zai kai ga mutuwa ba. A’a, sai dai don a ɗaukaka Allah a kuma ɗaukaka Ɗan Allah ta wurin wannan.” 5 Yesu kuwa yana ƙaunar Marta da ’yar’uwarta da kuma Lazarus. 6 Duk da haka sa’ad da ya ji Lazarus ba shi da lafiya, sai ya ƙara kwana biyu a inda yake. 7 Sai ya ce wa almajiransa, “Mu koma Yahudiya.” 8 Sai suka ce, “Rabbi, ba da daɗewa ba ne Yahudawa suka nemi su jajjefe ka, duk da haka za ka koma can?” 9 Yesu ya amsa ya ce, “Ba sa’a goma sha biyu ce yini guda ba? Mutumin da yake tafiya da rana ba zai yi tuntuɓe ba gama yana ganin hasken duniyan nan. 10 Sai a sa’ad da yake tafiya da dare ne zai yi tuntuɓe, don ba shi da haske.” 11 Bayan ya faɗa haka, sai ya ƙara ce musu, “Abokinmu Lazarus ya yi barci, amma za ni in tashe shi.” 12 Almajiransa suka ce, “Ubangiji, in barci ne yake, to, ai, zai sami sauƙi.” 13 Yesu kuwa yana magana mutuwarsa ce, amma almajiransa suka ɗauka yana nufin barcin gaskiya ne. 14 Saboda haka sai ya gaya musu a fili cewa, “Lazarus ya mutu, 15 amma saboda ku na yi farin ciki da ba na can, domin ku gaskata. Amma mu dai je wurinsa.” 16 Sai Toma (wanda ake kira Didaimus) ya ce wa sauran almajiran, “Mu ma mu je, mu mutu tare da shi.” 17 Da isowarsa, Yesu ya tarar Lazarus ya riga ya yi kwana huɗu a kabari. 18 Betani bai kai mil biyu ba daga Urushalima, 19 Yahudawa da yawa kuwa suka zo wurin Marta da Maryamu don su yi musu ta’aziyya, saboda rasuwar ɗan’uwansu. 20 Sa’ad da Marta ta ji cewa Yesu yana zuwa, sai ta fita don ta tarye shi, amma Maryamu ta zauna a gida. 21 Sai Marta ta ce wa Yesu, “Ubangiji, da kana nan da ɗan’uwana bai mutu ba. 22 Amma na san cewa ko yanzu ma Allah zai ba ka duk abin da ka roƙa.” 23 Yesu ya ce mata, “Ɗan’uwanki zai sāke tashi.” 24 Marta ta amsa ta ce, “Na sani zai sāke tashi a tashin matattu a rana ta ƙarshe.” 25 Yesu ya ce mata, “Ni ne tashin matattu da kuma rai. Duk wanda ya gaskata da ni zai rayu, ko ya mutu; 26 kuma duk wanda yake raye ya kuma gaskata da ni ba zai taɓa mutuwa ba. Kin gaskata wannan?” 27 Sai ta ce masa, “I, Ubangiji, na gaskata kai ne Kiristi, Ɗan Allah, mai zuwa cikin duniya.” 28 Bayan ta faɗa haka kuwa, sai ta koma ta je ta kira ’yar’uwarta Maryamu a gefe. Ta ce, “Ga Malam ya zo, kuma yana kiranki.” 29 Sa’ad da Maryamu ta ji haka sai ta yi wuf ta tafi wurinsa. 30 Yesu dai bai riga ya shiga ƙauyen ba tukuna, har yanzu yana inda Marta ta tarye shi. 31 Da Yahudawan da suke tare da Maryamu a cikin gida, suke mata ta’aziyya, suka ga ta yi wuf ta fita, sai suka bi ta, suna tsammani za tă kabarin ne tă yi kuka a can. 32 Sa’ad da Maryamu ta kai inda Yesu yake, ta kuma gan shi, sai ta fāɗi a gabansa ta ce, “Ubangiji, da kana nan, da ɗan’uwana bai mutu ba.” 33 Da Yesu ya ga tana kuka, Yahudawan da suka zo tare da ita ma suna kuka, sai ya yi juyayi ƙwarai a ruhu ya kuma damu. 34 Sai ya yi tambaya ya ce, “Ina kuka sa shi?”Suka amsa suka ce, “Ubangiji zo ka gani.” 35 Yesu ya yi kuka. 36 Sai Yahudawa suka ce, “Dubi yadda yake ƙaunarsa!” 37 Amma waɗansunsu suka ce, “Anya, wanda ya buɗe wa makahon nan idanu, ba zai iya yin wani abu yă hana wannan mutum mutuwa ba?” 38 Yesu, har yanzu cike da juyayi, ya zo kabarin. Kogo ne da aka rufe bakin da dutse. 39 Sai Yesu ya ce, “Ku kawar da dutsen.”Marta, ’yar’uwan mamacin ta ce, “Ubangiji, yanzu, ai, zai yi wari, don yau kwanansa huɗu ke nan a can.” 40 Sai Yesu ya ce, “Ban gaya miki cewa in kin gaskata za ki ga ɗaukakar Allah ba?” 41 Saboda haka suka kawar da dutsen. Sa’an nan Yesu ya dubi sama ya ce, “Uba, na gode maka da ka saurare ni. 42 Na san kullum kakan saurare ni, na dai faɗa haka ne saboda amfanin mutanen nan da suke tsaitsaye, don su gaskata cewa kai ka aiko ni.” 43 Sa’ad da ya faɗa haka, sai Yesu ya yi kira da babbar murya ya ce, “Lazarus, ka fito!” 44 Sai mamacin ya fito, hannuwansa da ƙafafunsa a daure da ƙyallayen lilin, fuskarsa kuwa an naɗe da mayafi.Yesu ya ce musu, “Ku tuɓe kayan bizo, ku bar shi yă tafi.” 45 Saboda haka Yahudawa da yawa da suka zo don su ziyarci Maryamu, suka kuma ga abin da Yesu ya yi, suka ba da gaskiya gare shi. 46 Amma waɗansunsu suka je wurin Farisiyawa suka gaya musu abin da Yesu ya yi. 47 Sai manyan firistoci da Farisiyawa suka kira taron Majalisa.Suka yi tambaya suna cewa, “Me muke yi ne? Ga mutumin nan yana yin abubuwan banmamaki masu yawa. 48 In fa muka ƙyale shi ya ci gaba da haka, kowa zai gaskata da shi, Romawa kuma su zo su karɓe wurinmu su kuma ƙwace ƙasarmu.” 49 Sai waninsu, mai suna Kayifas, wanda ya kasance babban firist a shekarar ya ce, “Ku dai ba ku san kome ba! 50 Ba ku gane ba, ai, gwamma mutum ɗaya yă mutu saboda mutane da duk ƙasar ta hallaka.” 51 Bai faɗa haka bisa nufinsa ba, sai dai a matsayinsa na babban firist a shekarar, ya yi annabci ne cewa Yesu zai mutu saboda ƙasar Yahudawa, 52 ba don ƙasan nan kaɗai ba amma don yă tattaro ’ya’yan Allah da suke warwatse ma, su zama ɗaya. 53 Saboda haka, daga wannan rana suka ƙulla su ɗauke ransa. 54 Saboda haka Yesu bai ƙara tafiya a cikin Yahudawa a sarari ba. A maimako haka sai ya janye zuwa yankin kusa da hamada, a wani ƙauye da ake kira Efraim, inda ya zauna da almajiransa. 55 Sa’ad da lokaci ya yi kusa a yi Bikin Ƙetarewa na Yahudawa, da yawa suka haura daga ƙauyuka zuwa Urushalima, don su tsarkake kansu kafin Bikin Ƙetarewa. 56 Suka yi ta neman Yesu, da suke a tsaitsaye a filin haikali kuwa suka dinga tambayar juna, suna cewa, “Me kuka gani? Anya, zai zo Bikin kuwa?” 57 Manyan firistoci da Farisiyawa tuni sun riga sun yi umarni cewa duk wanda ya san inda Yesu yake, yă faɗa don su kama shi.

In Other Versions

John 11 in the ANGEFD

John 11 in the ANTPNG2D

John 11 in the AS21

John 11 in the BAGH

John 11 in the BBPNG

John 11 in the BBT1E

John 11 in the BDS

John 11 in the BEV

John 11 in the BHAD

John 11 in the BIB

John 11 in the BLPT

John 11 in the BNT

John 11 in the BNTABOOT

John 11 in the BNTLV

John 11 in the BOATCB

John 11 in the BOATCB2

John 11 in the BOBCV

John 11 in the BOCNT

John 11 in the BOECS

John 11 in the BOGWICC

John 11 in the BOHCV

John 11 in the BOHLNT

John 11 in the BOHNTLTAL

John 11 in the BOICB

John 11 in the BOILNTAP

John 11 in the BOITCV

John 11 in the BOKCV

John 11 in the BOKCV2

John 11 in the BOKHWOG

John 11 in the BOKSSV

John 11 in the BOLCB

John 11 in the BOLCB2

John 11 in the BOMCV

John 11 in the BONAV

John 11 in the BONCB

John 11 in the BONLT

John 11 in the BONUT2

John 11 in the BOPLNT

John 11 in the BOSCB

John 11 in the BOSNC

John 11 in the BOTLNT

John 11 in the BOVCB

John 11 in the BOYCB

John 11 in the BPBB

John 11 in the BPH

John 11 in the BSB

John 11 in the CCB

John 11 in the CUV

John 11 in the CUVS

John 11 in the DBT

John 11 in the DGDNT

John 11 in the DHNT

John 11 in the DNT

John 11 in the ELBE

John 11 in the EMTV

John 11 in the ESV

John 11 in the FBV

John 11 in the FEB

John 11 in the GGMNT

John 11 in the GNT

John 11 in the HARY

John 11 in the HNT

John 11 in the IRVA

John 11 in the IRVB

John 11 in the IRVG

John 11 in the IRVH

John 11 in the IRVK

John 11 in the IRVM

John 11 in the IRVM2

John 11 in the IRVO

John 11 in the IRVP

John 11 in the IRVT

John 11 in the IRVT2

John 11 in the IRVU

John 11 in the ISVN

John 11 in the JSNT

John 11 in the KAPI

John 11 in the KBT1ETNIK

John 11 in the KBV

John 11 in the KJV

John 11 in the KNFD

John 11 in the LBA

John 11 in the LBLA

John 11 in the LNT

John 11 in the LSV

John 11 in the MAAL

John 11 in the MBV

John 11 in the MBV2

John 11 in the MHNT

John 11 in the MKNFD

John 11 in the MNG

John 11 in the MNT

John 11 in the MNT2

John 11 in the MRS1T

John 11 in the NAA

John 11 in the NASB

John 11 in the NBLA

John 11 in the NBS

John 11 in the NBVTP

John 11 in the NET2

John 11 in the NIV11

John 11 in the NNT

John 11 in the NNT2

John 11 in the NNT3

John 11 in the PDDPT

John 11 in the PFNT

John 11 in the RMNT

John 11 in the SBIAS

John 11 in the SBIBS

John 11 in the SBIBS2

John 11 in the SBICS

John 11 in the SBIDS

John 11 in the SBIGS

John 11 in the SBIHS

John 11 in the SBIIS

John 11 in the SBIIS2

John 11 in the SBIIS3

John 11 in the SBIKS

John 11 in the SBIKS2

John 11 in the SBIMS

John 11 in the SBIOS

John 11 in the SBIPS

John 11 in the SBISS

John 11 in the SBITS

John 11 in the SBITS2

John 11 in the SBITS3

John 11 in the SBITS4

John 11 in the SBIUS

John 11 in the SBIVS

John 11 in the SBT

John 11 in the SBT1E

John 11 in the SCHL

John 11 in the SNT

John 11 in the SUSU

John 11 in the SUSU2

John 11 in the SYNO

John 11 in the TBIAOTANT

John 11 in the TBT1E

John 11 in the TBT1E2

John 11 in the TFTIP

John 11 in the TFTU

John 11 in the TGNTATF3T

John 11 in the THAI

John 11 in the TNFD

John 11 in the TNT

John 11 in the TNTIK

John 11 in the TNTIL

John 11 in the TNTIN

John 11 in the TNTIP

John 11 in the TNTIZ

John 11 in the TOMA

John 11 in the TTENT

John 11 in the UBG

John 11 in the UGV

John 11 in the UGV2

John 11 in the UGV3

John 11 in the VBL

John 11 in the VDCC

John 11 in the YALU

John 11 in the YAPE

John 11 in the YBVTP

John 11 in the ZBP