John 19 (BOHCB)

1 Sa’an nan Bilatus ya tafi da Yesu ya kuma sa aka yi masa bulala. 2 Sai sojojin suka tuƙa rawanin ƙaya suka sa masa a kā, suka kuma yafa masa wata riga mai ruwan shunayya. 3 Suka yi ta zuwa wurinsa suna cewa, “Ranka yă daɗe, sarkin Yahudawa!” Suna ta marinsa a fuska. 4 Bilatus kuwa ya sāke fitowa ya ce wa Yahudawa, “Ga shi, zan fito muku da shi don ku san cewa ban same shi da wani abin zargi ba.” 5 Sa’ad da Yesu ya fito sanye da rawanin ƙayar da kuma riga mai ruwan shunayya, sai Bilatus ya ce musu, “Ga mutumin!” 6 Nan da nan da manyan firistoci da ma’aikatansu suka gan shi, sai suka yi ihu suka ce, “A gicciye! A gicciye!”Amma Bilatus ya amsa ya ce, “Ku, ku ɗauke shi ku gicciye. Ni dai ban same shi da wani abin zargi ba.” 7 Yahudawa dai suka nace suna cewa, “Mu fa muna da doka, kuma bisa ga dokar dole yă mutu domin ya mai da kansa Ɗan Allah.” 8 Da Bilatus ya ji haka, sai tsoro ya ƙara kama shi, 9 sai ya sāke koma cikin fada. Ya tambayi Yesu, “Daga ina ka fito?” Amma Yesu bai amsa masa ba. 10 Bilatus ya ce, “Ba za ka yi mini magana ba? Ba ka san cewa ina da ikon sakinka, ko gicciye ka ba?” 11 Yesu ya amsa ya ce, “Ba ka da wani iko a kaina, in ba a ba ka daga sama ba. Saboda haka wanda ya bashe ni gare ka, ya fi na zunubi.” 12 Daga nan fa, Bilatus ya yi nemi yă saki Yesu, sai dai Yahudawa suka yi ta ihu suna cewa, “In ka saki wannan mutum, kai ba abokin Kaisar ba ne. Duk wanda ya ɗauka kansa a matsayin sarki, ai, yana gāba da Kaisar ne.” 13 Da Bilatus ya ji haka, sai ya fito da Yesu, ya kuma zauna a kujerar shari’ar da ake ce da shi Daɓen Dutse (wanda a harshen Arameyik ana ce da shi Gabbata). 14 Ranar Shirye-shiryen Makon Bikin Ƙetarewa ce kuwa, wajen sa’a ta shida.Sai Bilatus ya ce wa Yahudawa, “Ga sarkinku.” 15 Amma suka yi ihu suka ce, “A yi da shi! A yi da shi! A gicciye shi!”Bilatus ya ce, “A! In gicciye sarkinku?”Sai manyan firistoci suka amsa suka ce, “Mu dai, ba mu da wani sarki sai Kaisar.” 16 A ƙarshe Bilatus ya ba da shi gare su a gicciye shi.Saboda haka sojoji suka tafi da Yesu. 17 Ɗauke da gicciyensa, ya kuwa fita zuwa wurin Ƙoƙon Kai (wanda a harshen Arameya ana ce da shi Golgota). 18 Nan suka gicciye shi tare da waɗansu mutum biyu, ɗaya a kowane gefe da Yesu a tsakiya. 19 Bilatus ya sa aka rubuta wata sanarwa aka kafa a kan gicciyen. Abin da aka rubuta kuwa shi ne,Yesu Banazare, Sarkin Yahudawa. 20 Yahudawa da yawa suka karanta wannan sanarwa, gama inda aka gicciye Yesu yana kusa da birni. An kuwa rubuta sanarwar da Arameyanci, Romanci da kuma Girik. 21 Sai manyan firistocin Yahudawa suka ce, “A’a! Kada ka rubuta, ‘Sarkin Yahudawa,’ ka dai rubuta, wannan mutum ya ce shi sarkin Yahudawa ne.” 22 Bilatus ya amsa ya ce, “Abin da na rubuta, na rubuta.” 23 Da sojojin suka gicciye Yesu, sai suka ɗibi tufafinsa suka kasa kashi huɗu, kowanne ya ɗauki kashi ɗaya. Suka kuma ɗauki taguwarsa, taguwar kuwa ba ɗinki, saƙa ɗaya ce gudanta daga sama har ƙasa. 24 Sai suka ce wa juna, “Kada mu yage ta, sai dai mu jefa ƙuri’a a kanta mu ga wanda zai ci.”Wannan ya faru ne don a cika nassin da ya ce,“Suka rarraba tufafina a junansu,suka kuma jefa ƙuri’a a kan rigata.”Abin da sojojin suka yi ke nan. 25 To, tsaye kusa da gicciyen Yesu kuwa akwai mahaifiyarsa, tare da ’yar’uwar mahaifiyarsa, Maryamu matar Kilofas, da kuma Maryamu Magdalin. 26 Sa’ad da Yesu ya ga mahaifiyarsa a can, da kuma almajirin nan da yake ƙauna tsaye kusa, sai ya ce wa mahaifiyarsa, “Mace, ga ɗanki,” 27 ga almajirin kuwa ya ce, “Ga mahaifiyarka.” Tun daga wannan lokaci fa almajirin nan ya kai ta gidansa. 28 Bayan haka, sanin cewa an cika kome, kuma domin a cika Nassi, sai Yesu ya ce, “Ina jin ƙishirwa.” 29 To, akwai wani tulun ruwan tsami ajiye a can, saboda haka suka jiƙa soso da shi, suka soka soson a sandan itacen hizzob, suka kai bakin Yesu. 30 Da ya tsotsi abin sha ɗin, sai Yesu ya ce, “An gama.” Da wannan fa, ya sunkuyar da kansa ya saki ruhunsa. 31 To, ranan nan fa, ranar Shirye-shirye ce, kashegari kuma muhimmin Asabbaci ne. Domin Yahudawa ba sa so a bar jikunan a kan gicciyoyi a Asabbaci, sai suka roƙi Bilatus a kakkarye ƙafafunsu kuma sauko da jikunan. 32 Sai sojoji suka zo suka karya ƙafafun mutum na farko da aka gicciye tare da Yesu, da kuma na ɗayan. 33 Amma sa’ad da suka zo kan Yesu suka tarar ya riga ya mutu, ba su karya ƙafafunsa ba. 34 A maimako, sai ɗaya daga cikin sojojin ya soki Yesu a gefe da māshi, nan take jini da ruwa suka fito. 35 Mutumin da ya gani ɗin shi ya ba da shaida, shaidarsa kuwa gaskiya ce. Ya san gaskiya yake faɗa, yana kuma ba da shaidar domin ku ma ku gaskata. 36 Waɗannan abubuwa sun faru don a cika Nassi ne cewa, “Ba ko ɗaya daga cikin ƙasusuwansa da za a karya,” 37 kuma kamar yadda wani Nassi ya ce, “Za su dubi wanda suka soka.” 38 Bayan haka, Yusuf mutumin Arimateya ya roƙi Bilatus a ba shi jikin Yesu. Yusuf dai almajirin Yesu ne, amma a ɓoye domin yana tsoron Yahudawa. Da izinin Bilatus, ya zo ya ɗauki jikin. 39 Yana tare da Nikodimus, wannan da ya taɓa zuwa wurin Yesu da dare. Nikodimus ya zo da mur da aloyes a gauraye, wajen awo ɗari. 40 Da ɗaukowar jikin Yesu, sai su biyun suka nannaɗe shi tare da kayan ƙanshi a cikin ƙyallayen lilin bisa ga al’adar Yahudawa ta jana’iza. 41 A inda aka gicciye Yesu, akwai wani lambu, a cikin lambun kuwa akwai sabon kabari, wanda ba a taɓa sa kowa ba. 42 Da yake ranan nan, ranar Shirye-shirye ce ta Yahudawa, kabarin kuma yana kusa, sai suka binne Yesu a can.

In Other Versions

John 19 in the ANGEFD

John 19 in the ANTPNG2D

John 19 in the AS21

John 19 in the BAGH

John 19 in the BBPNG

John 19 in the BBT1E

John 19 in the BDS

John 19 in the BEV

John 19 in the BHAD

John 19 in the BIB

John 19 in the BLPT

John 19 in the BNT

John 19 in the BNTABOOT

John 19 in the BNTLV

John 19 in the BOATCB

John 19 in the BOATCB2

John 19 in the BOBCV

John 19 in the BOCNT

John 19 in the BOECS

John 19 in the BOGWICC

John 19 in the BOHCV

John 19 in the BOHLNT

John 19 in the BOHNTLTAL

John 19 in the BOICB

John 19 in the BOILNTAP

John 19 in the BOITCV

John 19 in the BOKCV

John 19 in the BOKCV2

John 19 in the BOKHWOG

John 19 in the BOKSSV

John 19 in the BOLCB

John 19 in the BOLCB2

John 19 in the BOMCV

John 19 in the BONAV

John 19 in the BONCB

John 19 in the BONLT

John 19 in the BONUT2

John 19 in the BOPLNT

John 19 in the BOSCB

John 19 in the BOSNC

John 19 in the BOTLNT

John 19 in the BOVCB

John 19 in the BOYCB

John 19 in the BPBB

John 19 in the BPH

John 19 in the BSB

John 19 in the CCB

John 19 in the CUV

John 19 in the CUVS

John 19 in the DBT

John 19 in the DGDNT

John 19 in the DHNT

John 19 in the DNT

John 19 in the ELBE

John 19 in the EMTV

John 19 in the ESV

John 19 in the FBV

John 19 in the FEB

John 19 in the GGMNT

John 19 in the GNT

John 19 in the HARY

John 19 in the HNT

John 19 in the IRVA

John 19 in the IRVB

John 19 in the IRVG

John 19 in the IRVH

John 19 in the IRVK

John 19 in the IRVM

John 19 in the IRVM2

John 19 in the IRVO

John 19 in the IRVP

John 19 in the IRVT

John 19 in the IRVT2

John 19 in the IRVU

John 19 in the ISVN

John 19 in the JSNT

John 19 in the KAPI

John 19 in the KBT1ETNIK

John 19 in the KBV

John 19 in the KJV

John 19 in the KNFD

John 19 in the LBA

John 19 in the LBLA

John 19 in the LNT

John 19 in the LSV

John 19 in the MAAL

John 19 in the MBV

John 19 in the MBV2

John 19 in the MHNT

John 19 in the MKNFD

John 19 in the MNG

John 19 in the MNT

John 19 in the MNT2

John 19 in the MRS1T

John 19 in the NAA

John 19 in the NASB

John 19 in the NBLA

John 19 in the NBS

John 19 in the NBVTP

John 19 in the NET2

John 19 in the NIV11

John 19 in the NNT

John 19 in the NNT2

John 19 in the NNT3

John 19 in the PDDPT

John 19 in the PFNT

John 19 in the RMNT

John 19 in the SBIAS

John 19 in the SBIBS

John 19 in the SBIBS2

John 19 in the SBICS

John 19 in the SBIDS

John 19 in the SBIGS

John 19 in the SBIHS

John 19 in the SBIIS

John 19 in the SBIIS2

John 19 in the SBIIS3

John 19 in the SBIKS

John 19 in the SBIKS2

John 19 in the SBIMS

John 19 in the SBIOS

John 19 in the SBIPS

John 19 in the SBISS

John 19 in the SBITS

John 19 in the SBITS2

John 19 in the SBITS3

John 19 in the SBITS4

John 19 in the SBIUS

John 19 in the SBIVS

John 19 in the SBT

John 19 in the SBT1E

John 19 in the SCHL

John 19 in the SNT

John 19 in the SUSU

John 19 in the SUSU2

John 19 in the SYNO

John 19 in the TBIAOTANT

John 19 in the TBT1E

John 19 in the TBT1E2

John 19 in the TFTIP

John 19 in the TFTU

John 19 in the TGNTATF3T

John 19 in the THAI

John 19 in the TNFD

John 19 in the TNT

John 19 in the TNTIK

John 19 in the TNTIL

John 19 in the TNTIN

John 19 in the TNTIP

John 19 in the TNTIZ

John 19 in the TOMA

John 19 in the TTENT

John 19 in the UBG

John 19 in the UGV

John 19 in the UGV2

John 19 in the UGV3

John 19 in the VBL

John 19 in the VDCC

John 19 in the YALU

John 19 in the YAPE

John 19 in the YBVTP

John 19 in the ZBP