Romans 7 (BOHCB)
1 Ba ku sani ba, ’yan’uwa, ina magana ne fa da mutanen da suka san doka, cewa dokar tana da iko a kan mutum muddin yana a raye ne kawai. 2 Misali, bisa ga doka mace mai aure tana daure ga mijinta muddin mijin yana da rai, amma in mijinta ya mutu, an sake ta ke nan daga dokar aure. 3 Saboda haka fa, in ta auri wani yayinda mijinta yana raye, za a ce da ita mazinaciya. Amma in mijinta ya mutu, an sake ta ke nan daga wannan doka, ita kuwa ba mazinaciya ba ce, ko da yake ta auri wani. 4 Saboda haka ’yan’uwana, ku ma kun mutu ga dokar ta wurin jikin Kiristi, domin ku zama na wani, gare shi wanda aka tashe shi daga matattu, don mu ba da amfani ga Allah. 5 Gama sa’ad da halin mutuntaka yake mulkinmu, sha’awace-sha’awacen zunubi waɗanda dokar ta zuga sun yi ta aiki a jikunanmu, don mu ba da amfani wa mutuwa. 6 Amma yanzu, ta wurin mutuwa ga abin da dā ya daure mu, an sake mu daga dokar saboda mu yi hidima a sabuwar hanyar Ruhu, ba a tsohuwar hanyar rubutaccen ƙa’ida ba. 7 Me za mu ce ke nan? Dokar zunubi ce? Sam, ko kaɗan! Tabbatacce ai, da ban san mene ne zunubi ba in ba ta wurin doka ba. Gama da ban san mene ne ƙyashi yake ba tabbatacce in ba don doka ta ce, “Kada ka yi ƙyashi ba.” 8 Amma zunubi, da ya sami dama ta wurin umarnin nan, ya haifar a cikina kowane halin ƙyashi iri-iri. Gama in babu doka, zunubi matacce ne. 9 Dā kam ina da rai sa’ad da ban san doka ba; amma da umarni ya zo, sai zunubi ya zaburo da rai na kuma mutu. 10 Na gane cewa wannan umarnin da aka nufa ya kawo rai, a gaskiya ya jawo mutuwa ce. 11 Gama zunubi, da ya sami dama ta wurin umarni, sai ya ruɗe ni, kuma ta wurin umarnin kuwa ya kashe ni. 12 Saboda haka fa, dokar tana da tsarki, umarnin kuma yana da tsarki, su duka suna da adalci da kuma kyau. 13 Abin nan da yana mai kyau, zai kawo mini mutuwa? Ko kaɗan! Amma domin zunubi ya bayyana kansa a matsayin zunubi, sai ya haifar da mutuwa a cikina ta wurin abin da yake mai kyau, domin ta wurin umarnin nan zunubi ya fito da matuƙar muninsa. 14 Mun san cewa doka aba ce ta ruhu; amma ni ba na ruhu ba ne, an sayar da ni a matsayin bawa ga zunubi. 15 Ban gane abin da nake yi ba. Don abin da nakan so yi, ba shi nakan yi ba, sai dai abin da nake ƙi, shi nake yi. 16 In kuma na yi abin da ba na son yi, na yarda da cewa dokar aba ce mai kyau. 17 Kamar dai yadda yake, ba ni kaina nake yinsa ba, sai dai zunubin da yake zaune a cikina ne. 18 Gama na san cewa babu wani abin kirkin da yake zaune a cikina, wato, a mutuntakata. Gama sha’awar yin abu mai kyau kam ina da ita, sai dai ikon yin ne fa babu. 19 Gama abin da nake yi ba shi ne abu mai kyau da nake so in yi ba; a’a, mugun da ba na so in yi, shi ne nake ci gaba da yi. 20 To, in na yi abin da ba na so in yi, ba ni ba ne nake yinsa, sai dai zunubin nan da yake zaune a cikina. 21 Saboda haka na gane wannan ƙa’ida ce take aiki a cikina. Sa’ad da nake so in yi abu mai kyau, sai in ga cewa mugun nan ne nake yi. 22 Gama a ciki-cikina ina farin cikin da dokar Allah; 23 amma ina ganin wata doka tana aiki a gaɓoɓin jikina, tana yaƙi da dokar hankalina, tana kuma sa in zama ɗaurarren dokar zunubin da take aiki a gaɓoɓin jikina. 24 Kaitona! Wane ne zai cece ni daga wannan jiki mai mutuwa? 25 Godiya ga Allah ta wurin Yesu Kiristi Ubangijinmu!Saboda haka fa, ni kaina a cikin hankalina, ni bawa ne ga dokar Allah, amma a mutuntaka, ni bawa ne ga dokar zunubi.
In Other Versions
Romans 7 in the ANGEFD
Romans 7 in the ANTPNG2D
Romans 7 in the AS21
Romans 7 in the BAGH
Romans 7 in the BBPNG
Romans 7 in the BBT1E
Romans 7 in the BDS
Romans 7 in the BEV
Romans 7 in the BHAD
Romans 7 in the BIB
Romans 7 in the BLPT
Romans 7 in the BNT
Romans 7 in the BNTABOOT
Romans 7 in the BNTLV
Romans 7 in the BOATCB
Romans 7 in the BOATCB2
Romans 7 in the BOBCV
Romans 7 in the BOCNT
Romans 7 in the BOECS
Romans 7 in the BOGWICC
Romans 7 in the BOHCV
Romans 7 in the BOHLNT
Romans 7 in the BOHNTLTAL
Romans 7 in the BOICB
Romans 7 in the BOILNTAP
Romans 7 in the BOITCV
Romans 7 in the BOKCV
Romans 7 in the BOKCV2
Romans 7 in the BOKHWOG
Romans 7 in the BOKSSV
Romans 7 in the BOLCB
Romans 7 in the BOLCB2
Romans 7 in the BOMCV
Romans 7 in the BONAV
Romans 7 in the BONCB
Romans 7 in the BONLT
Romans 7 in the BONUT2
Romans 7 in the BOPLNT
Romans 7 in the BOSCB
Romans 7 in the BOSNC
Romans 7 in the BOTLNT
Romans 7 in the BOVCB
Romans 7 in the BOYCB
Romans 7 in the BPBB
Romans 7 in the BPH
Romans 7 in the BSB
Romans 7 in the CCB
Romans 7 in the CUV
Romans 7 in the CUVS
Romans 7 in the DBT
Romans 7 in the DGDNT
Romans 7 in the DHNT
Romans 7 in the DNT
Romans 7 in the ELBE
Romans 7 in the EMTV
Romans 7 in the ESV
Romans 7 in the FBV
Romans 7 in the FEB
Romans 7 in the GGMNT
Romans 7 in the GNT
Romans 7 in the HARY
Romans 7 in the HNT
Romans 7 in the IRVA
Romans 7 in the IRVB
Romans 7 in the IRVG
Romans 7 in the IRVH
Romans 7 in the IRVK
Romans 7 in the IRVM
Romans 7 in the IRVM2
Romans 7 in the IRVO
Romans 7 in the IRVP
Romans 7 in the IRVT
Romans 7 in the IRVT2
Romans 7 in the IRVU
Romans 7 in the ISVN
Romans 7 in the JSNT
Romans 7 in the KAPI
Romans 7 in the KBT1ETNIK
Romans 7 in the KBV
Romans 7 in the KJV
Romans 7 in the KNFD
Romans 7 in the LBA
Romans 7 in the LBLA
Romans 7 in the LNT
Romans 7 in the LSV
Romans 7 in the MAAL
Romans 7 in the MBV
Romans 7 in the MBV2
Romans 7 in the MHNT
Romans 7 in the MKNFD
Romans 7 in the MNG
Romans 7 in the MNT
Romans 7 in the MNT2
Romans 7 in the MRS1T
Romans 7 in the NAA
Romans 7 in the NASB
Romans 7 in the NBLA
Romans 7 in the NBS
Romans 7 in the NBVTP
Romans 7 in the NET2
Romans 7 in the NIV11
Romans 7 in the NNT
Romans 7 in the NNT2
Romans 7 in the NNT3
Romans 7 in the PDDPT
Romans 7 in the PFNT
Romans 7 in the RMNT
Romans 7 in the SBIAS
Romans 7 in the SBIBS
Romans 7 in the SBIBS2
Romans 7 in the SBICS
Romans 7 in the SBIDS
Romans 7 in the SBIGS
Romans 7 in the SBIHS
Romans 7 in the SBIIS
Romans 7 in the SBIIS2
Romans 7 in the SBIIS3
Romans 7 in the SBIKS
Romans 7 in the SBIKS2
Romans 7 in the SBIMS
Romans 7 in the SBIOS
Romans 7 in the SBIPS
Romans 7 in the SBISS
Romans 7 in the SBITS
Romans 7 in the SBITS2
Romans 7 in the SBITS3
Romans 7 in the SBITS4
Romans 7 in the SBIUS
Romans 7 in the SBIVS
Romans 7 in the SBT
Romans 7 in the SBT1E
Romans 7 in the SCHL
Romans 7 in the SNT
Romans 7 in the SUSU
Romans 7 in the SUSU2
Romans 7 in the SYNO
Romans 7 in the TBIAOTANT
Romans 7 in the TBT1E
Romans 7 in the TBT1E2
Romans 7 in the TFTIP
Romans 7 in the TFTU
Romans 7 in the TGNTATF3T
Romans 7 in the THAI
Romans 7 in the TNFD
Romans 7 in the TNT
Romans 7 in the TNTIK
Romans 7 in the TNTIL
Romans 7 in the TNTIN
Romans 7 in the TNTIP
Romans 7 in the TNTIZ
Romans 7 in the TOMA
Romans 7 in the TTENT
Romans 7 in the UBG
Romans 7 in the UGV
Romans 7 in the UGV2
Romans 7 in the UGV3
Romans 7 in the VBL
Romans 7 in the VDCC
Romans 7 in the YALU
Romans 7 in the YAPE
Romans 7 in the YBVTP
Romans 7 in the ZBP