Acts 20 (BOHCB)

1 Sa’ad da hayaniyar ta kwanta, sai Bulus ya aika a kira almajiran, kuma bayan ya ƙarfafa su, sai ya yi bankwana ya tafi Makidoniya. 2 Ya ratsa wurin yana ƙarfafa mutanen da kalmomi masu yawa, a ƙarshe kuma ya kai Giris, 3 inda ya zauna wata uku. Da yake Yahudawa sun ƙulla masa makirci, a lokacin da yake shirin tashi cikin jirgin ruwa zuwa Suriya, sai ya yanka shawara yă koma ta Makidoniya. 4 Sai Sofater ɗan Fairrus daga Bereya, Aristarkus da Sekundus daga Tessalonika, Gayus daga Derbe, Timoti ma, da Tikikus da Turofimus daga lardin Asiya suka tafi tare da shi. 5 Waɗannan mutane suka sha gaba suka kuma jira mu a Toruwas. 6 Amma muka tashi daga Filibbi a jirgin ruwa bayan Bikin Burodi Marar Yisti bayan kuma kwana biyar muka sadu da sauran a Toruwas, inda muka zauna kwana bakwai. 7 A ranar farko ta mako muka taru wuri ɗaya don gutsuttsura burodi. Bulus ya yi wa mutane magana, don yana niyyar tashi kashegari, sai ya yi ta yin magana har tsakar dare. 8 Akwai fitilu da yawa a ɗakin gidan saman da muka taru. 9 Akwai wani saurayi zaune a taga mai suna Yitikus, wanda barci mai nauyi ya ɗauke shi yayinda Bulus yake ta tsawaita magana. Sa’ad da yake barci, sai ya fāɗi daga gidan sama a hawa ta uku aka kuma ɗauke shi matacce. 10 Sai Bulus ya sauka, ya miƙe a kan saurayin ya rungume shi ya ce, “Kada ku damu, yana da rai!” 11 Sai ya koma ɗakin da yake a gidan sama, ya gutsuttsura burodi ya kuma ci. Bayan ya yi magana har gari ya waye, sai ya tafi. 12 Mutanen suka ɗauki saurayin da rai zuwa gida suka kuma ta’azantu ƙwarai da gaske. 13 Mu kuwa muka ci gaba zuwa jirgin ruwan muka tashi muka nufi Assos inda za mu ɗauki Bulus. Ya yi wannan shirin don zai tafi can da ƙafa. 14 Da ya same mu a Assos, sai muka ɗauke shi a jirgin ruwan muka zo Mitilen. 15 Kashegari muka tashi cikin jirgin ruwa daga can muka zo gefen Kiyos. Kwana ɗaya bayan wannan, sai muka ƙetare zuwa Samos, kashegari kuma muka iso Miletus. 16 Bulus ya yanke shawara yă wuce Afisa a jirgin ruwa don kada yă ɓata lokaci a lardin Asiya, gama yana sauri yă kai Urushalima, in ya yiwu ma, a ranar Fentekos. 17 Daga Miletus, Bulus ya aika zuwa Afisa a kira dattawan ikkilisiya. 18 Da suka iso, sai ya ce musu, “Kun san irin zaman da na yi tun lokacin da na zauna da ku, daga ranar farkon da na zo cikin lardin Asiya. 19 Na bauta wa Ubangiji da matuƙar tawali’u har da hawaye, da gwagwarmaya iri-irin da na sha game da makircin Yahudawa. 20 Kun san cewa ban yi wata-wata yin muku wa’azi game da duk abin da zai amfane ku ba amma na koyar da ku a fili da kuma gida-gida. 21 Na yi shela ga Yahudawa da Hellenawa cewa dole su juye ga Allah cikin tuba su kuma amince da Ubangijinmu Yesu. 22 “Yanzu kuma Ruhu ya tilasta ni, za ni Urushalima, ba tare da sanin abin da zai faru da ni a can ba. 23 Na dai san cewa a kowace birni Ruhu Mai Tsarki yakan gargaɗe ni cewa kurkuku da shan wuya suna jirana. 24 Amma ni ban ɗauki raina a bakin kome ba, in dai zan iya gama tserena in kuma kammala aikin da Ubangiji Yesu ya ba ni aikin shaida bisharar alherin Allah. 25 “Yanzu na san cewa ba ko ɗaya daga cikinku wanda na zazzaga ina muku wa’azin mulkin Allah da zai sāke ganina. 26 Saboda haka, ina muku shela a yau cewa ba ni da alhakin kowa a kaina. 27 Gama ban yi wata-wata a sanar muku dukan nufin Allah ba. 28 Ku lura da kanku da dukan garken da Ruhu Mai Tsarki ya sa ku ku zama masu kula da shi. Ku zama masu kiwon ikkilisiyar Allah, wadda ya saya da jininsa. 29 Na san cewa bayan na tafi, mugayen kyarketai za su shigo cikinku ba za su kuwa ƙyale garken ba. 30 Ko cikinku ma mutane za su taso su karkatar da gaskiya don su jawo wa kansu almajirai. 31 Saboda haka ku zauna a faɗake! Ku tuna cewa shekara uku, dare da rana ban taɓa fasa yin wa kowannenku gargaɗi ba, har da hawaye. 32 “To, yanzu na danƙa ku ga Allah da kuma ga maganar alherinsa, wadda za tă iya gina ku ta kuma ba ku gādo a cikin dukan waɗanda aka tsarkake. 33 Ban yi ƙyashin azurfa ko zinariya ko tufafin kowa ba. 34 Ku kanku kun san cewa hannuwan nan nawa sun biya mini bukatuna da kuma na abokan aikina. 35 Cikin kowane abin da na yi, na nuna muku cewa da irin wannan aiki tuƙuru don mu taimaki marasa ƙarfi, muna tunawa da kalmomin da Ubangiji Yesu kansa ya ce, ‘Bayarwa ta fi karɓa albarka.’ ” 36 Da ya faɗi haka, ya durƙusa tare da dukansu ya yi addu’a. 37 Sai dukansu suka yi kuka suka rungume shi, suka kuma yi masa sumba. 38 Abin da ya fi sa su baƙin ciki shi ne maganarsa da ya ce, ba za su ƙara ganin fuskarsa ba. Sai suka raka shi zuwa wajen jirgin ruwa.

In Other Versions

Acts 20 in the ANGEFD

Acts 20 in the ANTPNG2D

Acts 20 in the AS21

Acts 20 in the BAGH

Acts 20 in the BBPNG

Acts 20 in the BBT1E

Acts 20 in the BDS

Acts 20 in the BEV

Acts 20 in the BHAD

Acts 20 in the BIB

Acts 20 in the BLPT

Acts 20 in the BNT

Acts 20 in the BNTABOOT

Acts 20 in the BNTLV

Acts 20 in the BOATCB

Acts 20 in the BOATCB2

Acts 20 in the BOBCV

Acts 20 in the BOCNT

Acts 20 in the BOECS

Acts 20 in the BOGWICC

Acts 20 in the BOHCV

Acts 20 in the BOHLNT

Acts 20 in the BOHNTLTAL

Acts 20 in the BOICB

Acts 20 in the BOILNTAP

Acts 20 in the BOITCV

Acts 20 in the BOKCV

Acts 20 in the BOKCV2

Acts 20 in the BOKHWOG

Acts 20 in the BOKSSV

Acts 20 in the BOLCB

Acts 20 in the BOLCB2

Acts 20 in the BOMCV

Acts 20 in the BONAV

Acts 20 in the BONCB

Acts 20 in the BONLT

Acts 20 in the BONUT2

Acts 20 in the BOPLNT

Acts 20 in the BOSCB

Acts 20 in the BOSNC

Acts 20 in the BOTLNT

Acts 20 in the BOVCB

Acts 20 in the BOYCB

Acts 20 in the BPBB

Acts 20 in the BPH

Acts 20 in the BSB

Acts 20 in the CCB

Acts 20 in the CUV

Acts 20 in the CUVS

Acts 20 in the DBT

Acts 20 in the DGDNT

Acts 20 in the DHNT

Acts 20 in the DNT

Acts 20 in the ELBE

Acts 20 in the EMTV

Acts 20 in the ESV

Acts 20 in the FBV

Acts 20 in the FEB

Acts 20 in the GGMNT

Acts 20 in the GNT

Acts 20 in the HARY

Acts 20 in the HNT

Acts 20 in the IRVA

Acts 20 in the IRVB

Acts 20 in the IRVG

Acts 20 in the IRVH

Acts 20 in the IRVK

Acts 20 in the IRVM

Acts 20 in the IRVM2

Acts 20 in the IRVO

Acts 20 in the IRVP

Acts 20 in the IRVT

Acts 20 in the IRVT2

Acts 20 in the IRVU

Acts 20 in the ISVN

Acts 20 in the JSNT

Acts 20 in the KAPI

Acts 20 in the KBT1ETNIK

Acts 20 in the KBV

Acts 20 in the KJV

Acts 20 in the KNFD

Acts 20 in the LBA

Acts 20 in the LBLA

Acts 20 in the LNT

Acts 20 in the LSV

Acts 20 in the MAAL

Acts 20 in the MBV

Acts 20 in the MBV2

Acts 20 in the MHNT

Acts 20 in the MKNFD

Acts 20 in the MNG

Acts 20 in the MNT

Acts 20 in the MNT2

Acts 20 in the MRS1T

Acts 20 in the NAA

Acts 20 in the NASB

Acts 20 in the NBLA

Acts 20 in the NBS

Acts 20 in the NBVTP

Acts 20 in the NET2

Acts 20 in the NIV11

Acts 20 in the NNT

Acts 20 in the NNT2

Acts 20 in the NNT3

Acts 20 in the PDDPT

Acts 20 in the PFNT

Acts 20 in the RMNT

Acts 20 in the SBIAS

Acts 20 in the SBIBS

Acts 20 in the SBIBS2

Acts 20 in the SBICS

Acts 20 in the SBIDS

Acts 20 in the SBIGS

Acts 20 in the SBIHS

Acts 20 in the SBIIS

Acts 20 in the SBIIS2

Acts 20 in the SBIIS3

Acts 20 in the SBIKS

Acts 20 in the SBIKS2

Acts 20 in the SBIMS

Acts 20 in the SBIOS

Acts 20 in the SBIPS

Acts 20 in the SBISS

Acts 20 in the SBITS

Acts 20 in the SBITS2

Acts 20 in the SBITS3

Acts 20 in the SBITS4

Acts 20 in the SBIUS

Acts 20 in the SBIVS

Acts 20 in the SBT

Acts 20 in the SBT1E

Acts 20 in the SCHL

Acts 20 in the SNT

Acts 20 in the SUSU

Acts 20 in the SUSU2

Acts 20 in the SYNO

Acts 20 in the TBIAOTANT

Acts 20 in the TBT1E

Acts 20 in the TBT1E2

Acts 20 in the TFTIP

Acts 20 in the TFTU

Acts 20 in the TGNTATF3T

Acts 20 in the THAI

Acts 20 in the TNFD

Acts 20 in the TNT

Acts 20 in the TNTIK

Acts 20 in the TNTIL

Acts 20 in the TNTIN

Acts 20 in the TNTIP

Acts 20 in the TNTIZ

Acts 20 in the TOMA

Acts 20 in the TTENT

Acts 20 in the UBG

Acts 20 in the UGV

Acts 20 in the UGV2

Acts 20 in the UGV3

Acts 20 in the VBL

Acts 20 in the VDCC

Acts 20 in the YALU

Acts 20 in the YAPE

Acts 20 in the YBVTP

Acts 20 in the ZBP