Ephesians 5 (BOHCB)
1 Ku zama masu koyi da Allah, kamar ƙaunatattun ’ya’ya, 2 ku kuma yi rayuwar ƙauna, kamar yadda Kiristi ya ƙaunace mu, har ya ba da kansa dominmu a matsayin sadaka mai ƙanshi da kuma hadaya ga Allah. 3 Kada a ma ambaci fasikanci, da kowane irin aikin lalata, ko kwaɗayi a tsakaninku, domin bai dace da mutane masu tsarki na Allah ba. 4 Haka ma bai kamata a sami datti, ƙazamar magana, ko zancen banza a cikinku ba, domin ba su dace ba, a maimakon haka sai ku yi ta yin godiya. 5 Ku dai tabbata, ba wani mai fasikanci, ko mai aikin lalata, ko mai kwaɗayin (wanda shi da mai bautar gumaka ɗaya ne), da yake da gādo a mulkin Kiristi da na Allah. 6 Kada wani yă ruɗe ku da kalmomin wofi, gama saboda waɗannan abubuwa ne fushin Allah yake zuwa a kan marasa biyayya. 7 Saboda haka kada ku haɗa kai da su. 8 Gama a dā zukatanku sun cika da duhu, amma yanzu ku haske ne a cikin Ubangiji. Ku yi rayuwa kamar ’ya’yan haske 9 (domin amfanin haske ya ƙunshi nagarta, adalci, da kuma gaskiya) 10 ku nemi abin da zai gamshi Ubangiji. 11 Ku yi nesa da ayyukan duhun da mutane suke yi, a maimakon haka, ku tona su. 12 Gama abin kunya ne a ma faɗi abubuwan da marasa biyayya suke yi a ɓoye. 13 Duk abin da aka kawo a gaban haske ana iya ganinsa, kuma duk abin da aka haskaka yakan zama haske. 14 Shi ya sa aka ce,“Ka farka, ya kai mai barci,ka tashi daga matattu,Kiristi kuwa zai haskaka ka.” 15 Sai ku yi hankali sosai da yadda kuke rayuwa, kada ku zama kamar marasa hikima, sai dai kamar masu hikima. 16 Ku kuma yi matuƙar amfani da kowane zarafi, don kwanakin nan mugaye ne. 17 Saboda haka kada ku zama wawaye, sai dai ku fahimci ko mene ne nufin Ubangiji. 18 Kada ku bugu da ruwan inabi, wanda yake kai ga lalaci. A maimako haka, ku cika da Ruhu. 19 Ku yi zance da juna cikin zabura, da waƙoƙi, da kuma waƙoƙin ruhaniya. Ku rera, ku kuma yi kiɗe-kiɗe a zuciyarku ga Ubangiji. 20 Kullum ku dinga yin amfani da sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi, kuna gode wa Allah Uba a kome. 21 Ku yi biyayya da juna saboda bangirmar da kuke nuna wa Kiristi. 22 Matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, kamar ga Ubangiji ne kuke yi. 23 Gama miji shi ne kan mace, yadda Kiristi yake kai da kuma Mai Ceton ikkilisiya, wadda take jikinsa. 24 To, kamar yadda ikkilisiya take biyayya ga Kiristi, haka ma ya kamata mata su yi biyayya ga mazansu cikin kome. 25 Maza, ku ƙaunaci matanku, kamar yadda Kiristi ya ƙaunaci ikkilisiya, ya kuma ba da kansa dominta. 26 Ya mai da ikkilisiya ta zama mai tsarki ta wurin ikon maganarsa, ya kuma tsabtacce ta ta wurin wanke ta da ruwa. 27 Kiristi ya yi haka don yă miƙa wa kansa ikkilisiya mai ɗaukaka da kuma mai tsarki, marar aibi, marar tabo, da kuma marar lahani. 28 Don haka, dole maza su ƙaunaci matansu kamar yadda suke ƙaunar jikunansu. Wanda yake ƙaunar matarsa, yana ƙaunar kansa ne. 29 Gama ba wanda ya taɓa ƙin jikinsa, sai dai yă ciyar da shi, yă kuma kula da shi, kamar yadda Kiristi yake yi wa ikkilisiya, 30 gama mu gaɓoɓin jikinsa ne. 31 “Saboda haka mutum yakan bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, yă manne wa matarsa, su biyun su zama jiki ɗaya.” 32 Wannan babban asiri ne, amma na ɗauke shi a matsayin kwatanci ne na Kiristi da ikkilisiya. 33 Duk da haka, dole kowannenku yă ƙaunaci matarsa kamar yadda yake ƙaunar kansa, kuma dole matar tă yi biyayya ga mijinta.
In Other Versions
Ephesians 5 in the ANGEFD
Ephesians 5 in the ANTPNG2D
Ephesians 5 in the AS21
Ephesians 5 in the BAGH
Ephesians 5 in the BBPNG
Ephesians 5 in the BBT1E
Ephesians 5 in the BDS
Ephesians 5 in the BEV
Ephesians 5 in the BHAD
Ephesians 5 in the BIB
Ephesians 5 in the BLPT
Ephesians 5 in the BNT
Ephesians 5 in the BNTABOOT
Ephesians 5 in the BNTLV
Ephesians 5 in the BOATCB
Ephesians 5 in the BOATCB2
Ephesians 5 in the BOBCV
Ephesians 5 in the BOCNT
Ephesians 5 in the BOECS
Ephesians 5 in the BOGWICC
Ephesians 5 in the BOHCV
Ephesians 5 in the BOHLNT
Ephesians 5 in the BOHNTLTAL
Ephesians 5 in the BOICB
Ephesians 5 in the BOILNTAP
Ephesians 5 in the BOITCV
Ephesians 5 in the BOKCV
Ephesians 5 in the BOKCV2
Ephesians 5 in the BOKHWOG
Ephesians 5 in the BOKSSV
Ephesians 5 in the BOLCB
Ephesians 5 in the BOLCB2
Ephesians 5 in the BOMCV
Ephesians 5 in the BONAV
Ephesians 5 in the BONCB
Ephesians 5 in the BONLT
Ephesians 5 in the BONUT2
Ephesians 5 in the BOPLNT
Ephesians 5 in the BOSCB
Ephesians 5 in the BOSNC
Ephesians 5 in the BOTLNT
Ephesians 5 in the BOVCB
Ephesians 5 in the BOYCB
Ephesians 5 in the BPBB
Ephesians 5 in the BPH
Ephesians 5 in the BSB
Ephesians 5 in the CCB
Ephesians 5 in the CUV
Ephesians 5 in the CUVS
Ephesians 5 in the DBT
Ephesians 5 in the DGDNT
Ephesians 5 in the DHNT
Ephesians 5 in the DNT
Ephesians 5 in the ELBE
Ephesians 5 in the EMTV
Ephesians 5 in the ESV
Ephesians 5 in the FBV
Ephesians 5 in the FEB
Ephesians 5 in the GGMNT
Ephesians 5 in the GNT
Ephesians 5 in the HARY
Ephesians 5 in the HNT
Ephesians 5 in the IRVA
Ephesians 5 in the IRVB
Ephesians 5 in the IRVG
Ephesians 5 in the IRVH
Ephesians 5 in the IRVK
Ephesians 5 in the IRVM
Ephesians 5 in the IRVM2
Ephesians 5 in the IRVO
Ephesians 5 in the IRVP
Ephesians 5 in the IRVT
Ephesians 5 in the IRVT2
Ephesians 5 in the IRVU
Ephesians 5 in the ISVN
Ephesians 5 in the JSNT
Ephesians 5 in the KAPI
Ephesians 5 in the KBT1ETNIK
Ephesians 5 in the KBV
Ephesians 5 in the KJV
Ephesians 5 in the KNFD
Ephesians 5 in the LBA
Ephesians 5 in the LBLA
Ephesians 5 in the LNT
Ephesians 5 in the LSV
Ephesians 5 in the MAAL
Ephesians 5 in the MBV
Ephesians 5 in the MBV2
Ephesians 5 in the MHNT
Ephesians 5 in the MKNFD
Ephesians 5 in the MNG
Ephesians 5 in the MNT
Ephesians 5 in the MNT2
Ephesians 5 in the MRS1T
Ephesians 5 in the NAA
Ephesians 5 in the NASB
Ephesians 5 in the NBLA
Ephesians 5 in the NBS
Ephesians 5 in the NBVTP
Ephesians 5 in the NET2
Ephesians 5 in the NIV11
Ephesians 5 in the NNT
Ephesians 5 in the NNT2
Ephesians 5 in the NNT3
Ephesians 5 in the PDDPT
Ephesians 5 in the PFNT
Ephesians 5 in the RMNT
Ephesians 5 in the SBIAS
Ephesians 5 in the SBIBS
Ephesians 5 in the SBIBS2
Ephesians 5 in the SBICS
Ephesians 5 in the SBIDS
Ephesians 5 in the SBIGS
Ephesians 5 in the SBIHS
Ephesians 5 in the SBIIS
Ephesians 5 in the SBIIS2
Ephesians 5 in the SBIIS3
Ephesians 5 in the SBIKS
Ephesians 5 in the SBIKS2
Ephesians 5 in the SBIMS
Ephesians 5 in the SBIOS
Ephesians 5 in the SBIPS
Ephesians 5 in the SBISS
Ephesians 5 in the SBITS
Ephesians 5 in the SBITS2
Ephesians 5 in the SBITS3
Ephesians 5 in the SBITS4
Ephesians 5 in the SBIUS
Ephesians 5 in the SBIVS
Ephesians 5 in the SBT
Ephesians 5 in the SBT1E
Ephesians 5 in the SCHL
Ephesians 5 in the SNT
Ephesians 5 in the SUSU
Ephesians 5 in the SUSU2
Ephesians 5 in the SYNO
Ephesians 5 in the TBIAOTANT
Ephesians 5 in the TBT1E
Ephesians 5 in the TBT1E2
Ephesians 5 in the TFTIP
Ephesians 5 in the TFTU
Ephesians 5 in the TGNTATF3T
Ephesians 5 in the THAI
Ephesians 5 in the TNFD
Ephesians 5 in the TNT
Ephesians 5 in the TNTIK
Ephesians 5 in the TNTIL
Ephesians 5 in the TNTIN
Ephesians 5 in the TNTIP
Ephesians 5 in the TNTIZ
Ephesians 5 in the TOMA
Ephesians 5 in the TTENT
Ephesians 5 in the UBG
Ephesians 5 in the UGV
Ephesians 5 in the UGV2
Ephesians 5 in the UGV3
Ephesians 5 in the VBL
Ephesians 5 in the VDCC
Ephesians 5 in the YALU
Ephesians 5 in the YAPE
Ephesians 5 in the YBVTP
Ephesians 5 in the ZBP