John 20 (BOHCB)

1 Da sassafe a ranar farko ta mako, tun da sauran duhu, Maryamu Magdalin ta tafi kabarin ta kuwa tarar an kawar da dutsen daga bakin kabarin. 2 Sai ta zo da gudu wajen Siman Bitrus da ɗayan almajirin, wanda Yesu yake ƙauna, ta ce, “Sun ɗauke Ubangiji daga kabarin, ba mu kuma san inda suka sa shi ba!” 3 Sai Bitrus da almajirin nan suka nufi kabarin. 4 Dukansu biyu suna gudu, amma ɗayan almajirin ya tsere wa Bitrus ya kuma fara kai kabarin. 5 Ya sunkuya ya duba ciki ya ga ƙyallayen lilin ne kwance a can amma bai shiga ba. 6 Sa’an nan Siman Bitrus, wanda yake bayansa, ya iso ya kuwa wuce cikin kabarin. Ya ga ƙyallayen lilin kwance a can, 7 haka ma zanen binnewar da aka naɗe kan Yesu da shi. Zanen a naɗe yake shi kaɗai, a keɓe da lilin ɗin. 8 A ƙarshe sai almajirin nan, wanda ya kai kabarin da farko, shi ma ya shiga. Ya gani ya kuma gaskata. 9 (Har yanzu ba su fahimci Nassin nan da ya ce lalle ne Yesu yă tashi daga matattu ba.) 10 Sai almajiran suka koma zuwa inda suke zama. 11 Maryamu kuwa ta tsaya a bakin kabarin daga waje tana kuka. Da tana cikin kuka, sai ta sunkuya ta leƙa cikin kabarin, 12 sai ta ga waɗansu mala’iku biyu saye da fararen tufafi, zaune a inda dā gawar Yesu take, ɗaya wajen kai ɗayan kuma wajen ƙafafu. 13 Suka tambaye ta cewa, “Mace, don me kike kuka?”Ta ce, “Sun ɗauke Ubangijina, ban kuma san inda suka ajiye shi ba.” 14 Da ta faɗin haka, sai ta juya ta ga Yesu tsaye, sai dai ba tă gane cewa Yesu ne ba. 15 Sai ya ce, “Mace, don me kike kuka? Wa kike nema?”Ta yi tsammani shi ne mai aikin lambun, sai ta ce, “Ranka yă daɗe, in kai ne ka ɗauke shi, gaya mini inda ka ajiye shi, in je in ɗauke shi.” 16 Yesu ya ce mata, “Maryamu.”Sai ta juya wajensa ta ɗaga murya ta ce da Arameyanci, “Rabboni!” (Wanda yake nufin “Malam”). 17 Yesu ya ce, “Kada ki riƙe ni, gama ban riga na koma wajen Uba tukuna ba. A maimako, ki tafi wajen ’yan’uwana ki gaya musu, ‘Ina komawa wajen Ubana da Ubanku, wajen Allahna da kuma Allahnku.’ ” 18 Sai Maryamu Magdalin ta wajen almajiran da labari cewa, “Na ga Ubangiji!” Ta kuma gaya musu cewa ya faɗa mata waɗannan abubuwa. 19 Da Yamman ranar farko ta mako, sa’ad da almajiran suna tare, ƙofofi kuma suna a kulle saboda tsoron Yahudawa, sai ga Yesu ya zo ya tsaya a tsakiyarsu ya ce, “Salama tă kasance tare da ku!” 20 Bayan ya faɗa haka, sai ya nuna musu hannuwansa da gefensa. Sai almajiran suka yi farin ciki ƙwarai da suka ga Ubangiji. 21 Sai Yesu ya sāke ce musu, “Salama tă kasance tare da ku! Kamar yadda Uba ya aiko ni, haka ni ma ina aikan ku.” 22 Da wannan sai ya hura musu numfashinsa ya ce, “Ku karɓi Ruhu Mai Tsarki. 23 Duk wanda kuka gafarta wa zunubansa, an gafarta masa ke nan. Duk wanda ba ku gafarta wa ba kuwa, ba a gafarta masa ba ke nan.” 24 Toma kuwa (wanda ake kira Didaimus), ɗaya daga cikin Sha Biyun, ba ya tare da almajiran sa’ad da Yesu ya zo. 25 Saboda haka sauran almajiran suka ce masa, “Ai, mun ga Ubangiji!”Amma ya ce musu, “Ina, ai, sai na ga ramin ƙusa a hannuwansa na sa yatsata a inda ƙusoshi suka kasance, na kuma sa hannuna a gefensa, in ba haka ba, ba zan gaskata ba.” 26 Bayan mako guda, har wa yau almajiransa suna cikin gidan, Toma kuwa yana tare da su. Ko da yake ƙofofi suna kulle, sai ga Yesu ya zo ya tsaya a tsakiyarsu ya ce, “Salama tă kasance tare da ku!” 27 Sa’an nan ya ce wa Toma, “Sa yatsarka nan; dubi hannuwana. Miƙa hannunka ka sa a gefena. Ka daina shakka ka gaskata.” 28 Toma ya ce masa, “Ya Ubangijina da Allahna!” 29 Sai Yesu ya ce masa, “Wato ka gaskata saboda ka gan ni ne, masu albarka ne waɗanda ba su gan ni ba, amma suka gaskata.” 30 Yesu ya yi waɗansu abubuwan banmamaki da yawa a gaban almajiransa da ba a rubuta a wannan littafi ba. 31 An dai rubuta waɗannan ne don ku gaskata Yesu ne Kiristi, Ɗan Allah kuma ta wurin gaskatawa ku sami rai a cikin sunansa.

In Other Versions

John 20 in the ANGEFD

John 20 in the ANTPNG2D

John 20 in the AS21

John 20 in the BAGH

John 20 in the BBPNG

John 20 in the BBT1E

John 20 in the BDS

John 20 in the BEV

John 20 in the BHAD

John 20 in the BIB

John 20 in the BLPT

John 20 in the BNT

John 20 in the BNTABOOT

John 20 in the BNTLV

John 20 in the BOATCB

John 20 in the BOATCB2

John 20 in the BOBCV

John 20 in the BOCNT

John 20 in the BOECS

John 20 in the BOGWICC

John 20 in the BOHCV

John 20 in the BOHLNT

John 20 in the BOHNTLTAL

John 20 in the BOICB

John 20 in the BOILNTAP

John 20 in the BOITCV

John 20 in the BOKCV

John 20 in the BOKCV2

John 20 in the BOKHWOG

John 20 in the BOKSSV

John 20 in the BOLCB

John 20 in the BOLCB2

John 20 in the BOMCV

John 20 in the BONAV

John 20 in the BONCB

John 20 in the BONLT

John 20 in the BONUT2

John 20 in the BOPLNT

John 20 in the BOSCB

John 20 in the BOSNC

John 20 in the BOTLNT

John 20 in the BOVCB

John 20 in the BOYCB

John 20 in the BPBB

John 20 in the BPH

John 20 in the BSB

John 20 in the CCB

John 20 in the CUV

John 20 in the CUVS

John 20 in the DBT

John 20 in the DGDNT

John 20 in the DHNT

John 20 in the DNT

John 20 in the ELBE

John 20 in the EMTV

John 20 in the ESV

John 20 in the FBV

John 20 in the FEB

John 20 in the GGMNT

John 20 in the GNT

John 20 in the HARY

John 20 in the HNT

John 20 in the IRVA

John 20 in the IRVB

John 20 in the IRVG

John 20 in the IRVH

John 20 in the IRVK

John 20 in the IRVM

John 20 in the IRVM2

John 20 in the IRVO

John 20 in the IRVP

John 20 in the IRVT

John 20 in the IRVT2

John 20 in the IRVU

John 20 in the ISVN

John 20 in the JSNT

John 20 in the KAPI

John 20 in the KBT1ETNIK

John 20 in the KBV

John 20 in the KJV

John 20 in the KNFD

John 20 in the LBA

John 20 in the LBLA

John 20 in the LNT

John 20 in the LSV

John 20 in the MAAL

John 20 in the MBV

John 20 in the MBV2

John 20 in the MHNT

John 20 in the MKNFD

John 20 in the MNG

John 20 in the MNT

John 20 in the MNT2

John 20 in the MRS1T

John 20 in the NAA

John 20 in the NASB

John 20 in the NBLA

John 20 in the NBS

John 20 in the NBVTP

John 20 in the NET2

John 20 in the NIV11

John 20 in the NNT

John 20 in the NNT2

John 20 in the NNT3

John 20 in the PDDPT

John 20 in the PFNT

John 20 in the RMNT

John 20 in the SBIAS

John 20 in the SBIBS

John 20 in the SBIBS2

John 20 in the SBICS

John 20 in the SBIDS

John 20 in the SBIGS

John 20 in the SBIHS

John 20 in the SBIIS

John 20 in the SBIIS2

John 20 in the SBIIS3

John 20 in the SBIKS

John 20 in the SBIKS2

John 20 in the SBIMS

John 20 in the SBIOS

John 20 in the SBIPS

John 20 in the SBISS

John 20 in the SBITS

John 20 in the SBITS2

John 20 in the SBITS3

John 20 in the SBITS4

John 20 in the SBIUS

John 20 in the SBIVS

John 20 in the SBT

John 20 in the SBT1E

John 20 in the SCHL

John 20 in the SNT

John 20 in the SUSU

John 20 in the SUSU2

John 20 in the SYNO

John 20 in the TBIAOTANT

John 20 in the TBT1E

John 20 in the TBT1E2

John 20 in the TFTIP

John 20 in the TFTU

John 20 in the TGNTATF3T

John 20 in the THAI

John 20 in the TNFD

John 20 in the TNT

John 20 in the TNTIK

John 20 in the TNTIL

John 20 in the TNTIN

John 20 in the TNTIP

John 20 in the TNTIZ

John 20 in the TOMA

John 20 in the TTENT

John 20 in the UBG

John 20 in the UGV

John 20 in the UGV2

John 20 in the UGV3

John 20 in the VBL

John 20 in the VDCC

John 20 in the YALU

John 20 in the YAPE

John 20 in the YBVTP

John 20 in the ZBP