Revelation 18 (BOHCB)

1 Bayan wannan sai na ga wani mala’ika yana saukowa daga sama. Yana da iko mai girma, aka haskaka duniya da darajarsa. 2 Ya yi kira da babbar murya ya ce,“Ta fāɗi! Babilon Mai Girma ta fāɗi.Ta zama gidan aljanuda kuma wurin zaman kowace irin mugun ruhu,wurin zaman kowane irin tsuntsu marar tsabta da mai banƙyama. 3 Gama dukan al’ummai sun sha ruwan inabinhaukan zinace zinacenta.Sarakunan duniya sun yi zina tare da ita,attajiran duniya kuma sun arzuta da almubazzarancinta.” 4 Sai na ji wata murya daga sama ta ce,“Ku fita daga cikinta, mutanena,don kada zunubanta su shafe ku,don kada wata annobarta ta same ku; 5 gama zunubanta sun yi tsororuwa sun kai sama.Allah kuma ya tuna da laifofinta. 6 Ku sāka mata kamar yadda ta sāka muku;ku sāka mata sau biyu na abin da ta yi.Ku dama mata sau biyu na abin da yake cikin kwaf nata. 7 Ku ba ta isashen azaba da baƙin cikikamar daraja da kuma jin daɗin da ta ba wa kanta.A zuciyarta takan yi taƙama, ta ce,‘Ina zama kamar sarauniya;ni ba gwauruwa ba ce,kuma ba zan taɓa yin makoki ba.’ 8 Saboda haka a rana ɗaya annobarta za su cim mata,mutuwa, makoki da kuma yunwa.Wuta zai cinye ta,gama Ubangiji Allah mai girma ne, wanda yake shari’anta ta. 9 “Sa’ad da sarakunan duniya da suka yi zina da ita suka kuma yi tarayya cikin jin daɗinta suka ga hayaƙin ƙunarta, za su yi kuka da makoki saboda ita. 10 Don tsoron ganin azabarta za su tsaya daga nesa, su yi kuka suna cewa,“ ‘Kaito! Kaito, ya birni mai girma.Ya ke Babilon, birni mai iko!Cikin sa’a guda hallakarki ta zo!’ 11 “Attajiran duniya za su yi kuka su kuma yi makoki a kanta, domin ba wanda yake ƙara sayen kayayyakinsu 12 kayayyakin zinariya, azurfa, duwatsu masu daraja da lu’ulu’ai; lallausan lilin, tufa masu ruwan shunayya, siliki da jan tufa; da kowane irin katakai masu ƙanshi da kayayyaki na kowane iri da aka yi da hauren giwa, katakai masu tsada, tagulla, baƙin ƙarfe da dutse mai sheƙi; 13 kayayyakin sinnamon da kayan yaji, na turaren wuta, mur da turare, na ruwan inabi da man zaitun, na gari mai laushi da alkama; shanu da tumaki; dawakai da kekunan doki, da jikuna da kuma rayukan mutane. 14 “Za su ce, ‘Amfanin da kike marmari ya kuɓuce. Dukan arzikinki da darajarki sun ɓace, ba kuwa za a ƙara samunsu ba.’ 15 Attajiran da suka sayar da waɗannan kayayyaki suka kuma sami arzikinsu daga gare ta za su tsaya daga nesa, cike da tsoron ganin azabarta. Za su yi kuka da makoki 16 su ce,“ ‘Kaito! Kaito, ya birni mai girma,saye da lallausan lilin, shunayya da kuma ja,mai walƙiya da zinariya, duwatsu masu daraja da kuma lu’ulu’ai! 17 Cikin sa’a guda irin wannan dukiya mai yawa ta hallaka!’“Duk matuƙan jirgin ruwa, da dukan waɗanda suke tafiya a jirgin ruwa, ma’aikatanta, da duk masu samun abin zama gari daga teku za su tsaya daga nesa. 18 Sa’ad da suka ga hayaƙin ƙunarta, za su yi ihu su ce, ‘An taɓa samun birni kamar wannan babban birnin kuwa?’ 19 Za su zuba ƙura a kawunansu, da kuka da makoki za su yi ta kururuwa,“ ‘Kaito! Kaito, ya birni mai girma,inda dukan waɗanda suke da jiragen ruwa a tekusuka arzuta da ɗumbun dukiyarsa!Cikin sa’a ɗaya ta hallaka!’ 20 “Ki yi murna a kanta, ya sama!Ku yi murna, ku tsarkaka!Ku yi murna, ku manzanni da annabawa!Allah ya hukunta shisaboda abin da ya yi muku.” 21 Sa’an nan wani mala’ika mai ƙarfi ya ɗauki dutse kamar girman babban dutsen niƙa ya jefa cikin teku ya ce,“Da wannan irin giggitawaza a jefar da birnin Babilon mai girma ƙasa,ba za a ƙara ganin ta ba. 22 Ba za a ƙara jinƙarar kiɗin masu garaya da muryar mawaƙa, da na masu bushe-bushe, da na masu busan ƙahoa cikinki ba.Ba za a ƙara samun ma’aikaci na kowace irin sana’aa cikinki kuma ba.Ba za a ƙara jin ƙarar dutsen niƙaa cikinki kuma ba. 23 Hasken fitila ba zai ƙara haskakawaa cikinki ba.Ba za a ƙara jin muryar ango da amaryaa cikinki ba.Attajiranki, dā su ne manyan mutanen duniya.Ta wurin sihirinki, dukan ƙasashe sun kauce. 24 A cikinta aka sami jinin annabawa, da na tsarkaka,da kuma na dukan waɗanda aka kashe a duniya.”

In Other Versions

Revelation 18 in the ANGEFD

Revelation 18 in the ANTPNG2D

Revelation 18 in the AS21

Revelation 18 in the BAGH

Revelation 18 in the BBPNG

Revelation 18 in the BBT1E

Revelation 18 in the BDS

Revelation 18 in the BEV

Revelation 18 in the BHAD

Revelation 18 in the BIB

Revelation 18 in the BLPT

Revelation 18 in the BNT

Revelation 18 in the BNTABOOT

Revelation 18 in the BNTLV

Revelation 18 in the BOATCB

Revelation 18 in the BOATCB2

Revelation 18 in the BOBCV

Revelation 18 in the BOCNT

Revelation 18 in the BOECS

Revelation 18 in the BOGWICC

Revelation 18 in the BOHCV

Revelation 18 in the BOHLNT

Revelation 18 in the BOHNTLTAL

Revelation 18 in the BOICB

Revelation 18 in the BOILNTAP

Revelation 18 in the BOITCV

Revelation 18 in the BOKCV

Revelation 18 in the BOKCV2

Revelation 18 in the BOKHWOG

Revelation 18 in the BOKSSV

Revelation 18 in the BOLCB

Revelation 18 in the BOLCB2

Revelation 18 in the BOMCV

Revelation 18 in the BONAV

Revelation 18 in the BONCB

Revelation 18 in the BONLT

Revelation 18 in the BONUT2

Revelation 18 in the BOPLNT

Revelation 18 in the BOSCB

Revelation 18 in the BOSNC

Revelation 18 in the BOTLNT

Revelation 18 in the BOVCB

Revelation 18 in the BOYCB

Revelation 18 in the BPBB

Revelation 18 in the BPH

Revelation 18 in the BSB

Revelation 18 in the CCB

Revelation 18 in the CUV

Revelation 18 in the CUVS

Revelation 18 in the DBT

Revelation 18 in the DGDNT

Revelation 18 in the DHNT

Revelation 18 in the DNT

Revelation 18 in the ELBE

Revelation 18 in the EMTV

Revelation 18 in the ESV

Revelation 18 in the FBV

Revelation 18 in the FEB

Revelation 18 in the GGMNT

Revelation 18 in the GNT

Revelation 18 in the HARY

Revelation 18 in the HNT

Revelation 18 in the IRVA

Revelation 18 in the IRVB

Revelation 18 in the IRVG

Revelation 18 in the IRVH

Revelation 18 in the IRVK

Revelation 18 in the IRVM

Revelation 18 in the IRVM2

Revelation 18 in the IRVO

Revelation 18 in the IRVP

Revelation 18 in the IRVT

Revelation 18 in the IRVT2

Revelation 18 in the IRVU

Revelation 18 in the ISVN

Revelation 18 in the JSNT

Revelation 18 in the KAPI

Revelation 18 in the KBT1ETNIK

Revelation 18 in the KBV

Revelation 18 in the KJV

Revelation 18 in the KNFD

Revelation 18 in the LBA

Revelation 18 in the LBLA

Revelation 18 in the LNT

Revelation 18 in the LSV

Revelation 18 in the MAAL

Revelation 18 in the MBV

Revelation 18 in the MBV2

Revelation 18 in the MHNT

Revelation 18 in the MKNFD

Revelation 18 in the MNG

Revelation 18 in the MNT

Revelation 18 in the MNT2

Revelation 18 in the MRS1T

Revelation 18 in the NAA

Revelation 18 in the NASB

Revelation 18 in the NBLA

Revelation 18 in the NBS

Revelation 18 in the NBVTP

Revelation 18 in the NET2

Revelation 18 in the NIV11

Revelation 18 in the NNT

Revelation 18 in the NNT2

Revelation 18 in the NNT3

Revelation 18 in the PDDPT

Revelation 18 in the PFNT

Revelation 18 in the RMNT

Revelation 18 in the SBIAS

Revelation 18 in the SBIBS

Revelation 18 in the SBIBS2

Revelation 18 in the SBICS

Revelation 18 in the SBIDS

Revelation 18 in the SBIGS

Revelation 18 in the SBIHS

Revelation 18 in the SBIIS

Revelation 18 in the SBIIS2

Revelation 18 in the SBIIS3

Revelation 18 in the SBIKS

Revelation 18 in the SBIKS2

Revelation 18 in the SBIMS

Revelation 18 in the SBIOS

Revelation 18 in the SBIPS

Revelation 18 in the SBISS

Revelation 18 in the SBITS

Revelation 18 in the SBITS2

Revelation 18 in the SBITS3

Revelation 18 in the SBITS4

Revelation 18 in the SBIUS

Revelation 18 in the SBIVS

Revelation 18 in the SBT

Revelation 18 in the SBT1E

Revelation 18 in the SCHL

Revelation 18 in the SNT

Revelation 18 in the SUSU

Revelation 18 in the SUSU2

Revelation 18 in the SYNO

Revelation 18 in the TBIAOTANT

Revelation 18 in the TBT1E

Revelation 18 in the TBT1E2

Revelation 18 in the TFTIP

Revelation 18 in the TFTU

Revelation 18 in the TGNTATF3T

Revelation 18 in the THAI

Revelation 18 in the TNFD

Revelation 18 in the TNT

Revelation 18 in the TNTIK

Revelation 18 in the TNTIL

Revelation 18 in the TNTIN

Revelation 18 in the TNTIP

Revelation 18 in the TNTIZ

Revelation 18 in the TOMA

Revelation 18 in the TTENT

Revelation 18 in the UBG

Revelation 18 in the UGV

Revelation 18 in the UGV2

Revelation 18 in the UGV3

Revelation 18 in the VBL

Revelation 18 in the VDCC

Revelation 18 in the YALU

Revelation 18 in the YAPE

Revelation 18 in the YBVTP

Revelation 18 in the ZBP